'Ku Kashe 30, Fiye da Haka Su Taso': Tantirin Dan Bindiga Ya Yi Gargadi Ana tsaka da Sulhu
- An sake zama da yan bindiga a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma a Najeriya domin samun zaman lafiya a wasu yankuna
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa an samu halin tattaunawa da maharan ne a karamar hukumar Matazu da ke jihar
- Kachalla Ummaru ya gargadi jami’an tsaro cewa kashe ’yan bindiga 10 zai kawo bayyanar sababbi 20, har a birane da kauyuka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Matazu, Katsina - Karamar Matazu da ke jihar Katsina ta shiga jerin kananan hukumomi da ake sulhu da yan bindiga domin zaman lafiya.
An yi ganawar tsakanin shugabannin yankin da kuma yan bindiga a karamar hukumar domin dakile yawan hare-haren yan ta'adda.

Source: Twitter
Rahoton Zagazola Makama ya ce dukan bangarorin sun bukaci hakuri da kuma mutunta zaman sulhun da aka yi.

Kara karanta wannan
Katsina: Bayan Kachallah Isiya, tantirin ɗan bindiga ya cika alkawari domin mutunta sulhu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kananan hukumomi da suka yi sulhu da yan bindiga
Wannan na zuwa ne yayin da wasu kananan hukumomi a Katsina suka amince da sulhu da miyagun madadin amfani da karfin soja.
Mutanen wasu yankuna da dama suna yaba tsarin sulhun da ake yi da cewa yana haifar da 'da mai ido kuma suna ganin fa'idar haka.
Kananan hukumomin Batsari, Danmusa da Jibia da Faskari da kuma karamar hukumar Matazu duk sun yi sulhu da yan bindiga.

Source: Original
Dan bindiga ya gargadi hukumomi a Katsina
Fitaccen dan bindiga a yankin, Kachalla Ummaru, ya fito fili ya yi gargadi musamman ga hukumomin kan amfani da karfin soja.
Ummaru ya ce duk wani yunƙurin gwamnati na kashe ’yan bindiga 10, zai jawo sababbi 20 su fito domin ramawa.
Ya kara da cewa:
“Ku kashe 30 kuma, da dama za su sake bayyana, a cikin birane da kuma kauyuka wanda ba zai haifar da 'da mai ido ba."
Ummaru ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar yayin tattaunawar zaman lafiya da aka gudanar tsakanin ’yan bindiga da shugabannin al’umma a Matazu.
Rokon da aka yi ga yan bindiga, hukumomi
Ya gargadi jami’an tsaro da su daina kai hare-hare, yana mai jaddada cewa tattaunawar sulhu ba za ta yi tasiri ba sai an yi hakuri.
An gudanar da wannan taro ne domin haɓaka zaman lafiya da sulhu, wanda ya biyo bayan ƙoƙarin dakile matsalar ’yan bindiga a Katsina da jihohin makwabta.
Dattawan al’umma da suka halarci tattaunawar sun roƙi ’yan bindiga da jami’an tsaro su jajirce wajen kawo sahihin zaman lafiya ga al’ummar yankin.
Yan bindiga sun fara sakin mutane a Katsina
Kun ji cewa maganar sulhu da yan bindiga don zaman lafiya na ci gaba da sauya salo a wasu yankunan jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.
An gudanar da zaman sulhu a kwanan nan a karamar hukumar Faskari da dan bindiga, Ado Aliero domin samun zaman lafiya a yankunan.
Wasu daga cikin wadanda aka yi sulhu da su sun fara sakin mutanen da ke hannunsu saboda mutunta tsarin da tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
