Ana batun Sulhu, Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Katsina

Ana batun Sulhu, Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Katsina

  • Dakarun sojojin Najeriya sun gwabza fada da 'yan bindiga bayan sun kai wani hari a wasu kauyukan jihar Katsina
  • Sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sanda da jami'an rundunar C-Watch sun samu nasarar dakile harin na 'yan bindiga
  • Sai dai, harin ya yi sanadiyyar rasa ran mutum guda bayan 'yan bindiga sun haddasa hatsari da su ke tserewa daga yankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina.

Dakarun sojojin sun dakile harin na 'yan bindigan ne a kauyukan Awari Yashe da Sararawa na karamar hukumar Kusada da safiyar ranar Alhamis.

Sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga a Katsina
Hoton shugaban sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede da gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: @HQNigerianArmy, @dikko_radda
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Jagoran 'yan bindiga ya fara cika alkawari kan yarjejeniyar sulhu a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga su ka kai hari a Katsina

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin larfe 3:25 na dare, lokacin da wata tawagar da ake zargin ta ‘yan bindiga ce su ka mamaye kauyukan.

Dakarun sojoji tare da ‘yan sanda da jami'an rundunar C-Watch, sun yi gaggawar isa wajen, inda suka yi musayar wuta da maharan.

Majiyoyin sun bayyana cewa a lokacin musayar wutar, wani mazaunin yankin mai suna Sama’ila Dahiru, mai shekara 40, ya samu raunukan harbin bindiga, yayin da maharan su ka sace wani adadi mai yawa na dabbobi.

Hakazalika, majiyoyin sun kara da cewa a yayin tserewarsu ta hanyar Gidan Mutum Daya-Kofa, maharan sun haddasa wani mummunan hatsarin mota wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da ba a gano sunansa ba.

“Dukkan waɗanda abin ya rutsa da su an garzaya da su zuwa asibitin gwamnati na Kankia, inda likita ya tabbatar da mutuwar wanda ya rasu."

Kara karanta wannan

'Yan fansho sun fusata, suna shirin fara zanga zanga tsirara a fadin Najeriya

- Wata majiya

Majiyar ta tabbatar da cewa an kara kaimi wajen bin sawun maharan da suka tsere tare da dawo da dabbobin da aka sace, yayin da aka karfafa sintiri a yankin domin hana sake faruwar irin wannan hari.

'Yan bindiga sun farmaki wasu kauyuka a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kamal Musa ya shaidawa Legit Hausa akwai yankunan da 'yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a Katsina.

"An bar mutanen nan suna yin abin da su ka ga dama, su kashe na kashewa sannan su sace na sacewa."
"Ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kanta na al'umma.

- Kamal Musa

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun sace ƴar NYSC da ɗalibar jami'a, suna neman N50m

Jagoran 'yan bindiga ya sako mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran 'yan bindiga, Isiya Akwashi Garwa, ya fara cika alkawari kan yarjejeniyar sulhu a Katsina.

Isiya Akwashi Garwa ya sako mutane 28 da ke tsare a hannunsa don mutunta yarjejeniyar sulhu da aka kulla da shi a karamar hukumar Faskari.

Sako mutanen na zuwa ne bayan an yi wani zaman sulhu da aka yi da jagororin 'yan bindiga don samun zaman lafiya a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng