Zanga Zanga Ta Yi Zafi, Hedikwatar Tsaro Ta ba Tsofaffin Sojoji Umarni a Abuja

Zanga Zanga Ta Yi Zafi, Hedikwatar Tsaro Ta ba Tsofaffin Sojoji Umarni a Abuja

  • Yayin da tsofaffin sojojin Najeriya ke zanga-zanga a Abuja, Hedikwatar tsaro ta tsoma baki inda ta gargadi dattawan
  • Rundunar ta nuna damuwa kan yadda masu zanga-zangar suka mamaye ma'aikatar kudi da ke birnin tarayya watau Abuja
  • Hedikwatar a bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga sabon tsarin albashi da aka gabatar a 2024 bayan aiwatar da mafi ƙarancin albashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hedikwatar tsaro ta nuna damuwa game da zanga-zanga da tsofaffin sojoji ke ci gaba da yi a birnin Abuja.

Tsofaffin sojojin sun mamaye ma'aikatar kudi da ke Abuja domin neman a biya su hakkokinsu da aka rike musu.

Rundunar ta uamrci tsofaffin sojoji su watse a wurin zanga-zanga
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Umarnin da hedikwatar tsaro ta ba tsofaffin sojoji

Daily Trust ta ce rundunar ta umarci tsofaffin sojojin da ke zanga-zanga a Ma’aikatar da su bar wurin don bai wa gwamnati damar aiki.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga bayan an yi gumurzu a Katsina

Rahotanni sun nuna cewa tsofaffin sojojin da suka bar aikin soja a 2024 sun dawo kan titi bayan zanga-zangar watan da ya gabata.

Masu zanga-zangar sun koka cewa gwamnati ta gaza biyan hakkokinsu, suna mai cewa an yi watsi da su tsawon lokaci ba tare da kulawa ba.

Daraktan yaɗa labarai, Markus Kangye, ya ce an wayar da kan tsofaffin sojojin amma sun nace suna ci gaba da zanga-zanga.

Ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga tsarin albashi biyu da aka ƙirƙira a 2024 bayan gabatar da sabon mafi ƙarancin albashi.

Kangye ya ce akwai tsare-tsare na mafi karancin albashi daga Janairu 1 zuwa Yuli 28, 2024 sannan tsarin ya fara aiki daga Yuli 29.

Ya ƙara da cewa matakin tsofaffin sojojin na kawo cikas ga ayyukan Ma’aikatar Kuɗi, duk da cewa suna da damar yin zanga-zanga cikin lumana.

Ya ce:

“Dole a yi taka-tsantsan kuma a bar wurin domin barin gwamnati ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Zanga-zangar tsofaffin sojoji ta yi zafi a Abuja
Ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Alkawarin sojoji ga taimakawa gwamnati

Kangye ya nanata cewa rundunar za ta ci gaba da kare martabar ƙasar, taimakawa gwamnati wajen tsaron cikin gida da tabbatar da zaman lafiya.

Ya kuma fayyace cewa hakkokin tsofaffin sojoji na dogara da tsarin albashi da yake aiki a ranar da suka yi ritaya kawai.

Har ila yau, ya ce wadanda suka yi ritaya kafin Yuli 29, 2024 suna son a lissafa hakkokinsu bisa sabon tsari, amma hakan ba zai yiwu ba, cewar Daily Post.

Kangye ya jaddada cewa an yi musu bayanai akai-akai, amma sun ci gaba da hana mutane shiga ma’aikatar da kuma gudanar da zanga-zanga.

Tsofaffin sojoji sun yi zanga-zanga a Abuja

A baya, mun ba ku labarin cewa tsofaffin sojoji sun mamaye hedikwatar ma’aikatar kudi a Abuja domin neman hakkokinsu.

Tsofaffin sojojin sun ce an dakatar da albashinsu, an zabtare giratutinsu, kuma an hana su inshora tun bayan ajiye aikinsu.

Shugabanninsu sun ce ba za su bar wajen ba sai an biya musu bukatunsu gaba daya, yayin da rundunar sojoji ta ki yin martani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.