An Nemi Majalisa Ta Sauya Dokar Najeriya, Ta Sanyawa Musulmai Hutun Aiki Ranar Juma’a

An Nemi Majalisa Ta Sauya Dokar Najeriya, Ta Sanyawa Musulmai Hutun Aiki Ranar Juma’a

  • MURIC ta bayyana bukatar a bude kotunan shari’a a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan don amfanin Musulmai a yankin
  • Hakazalika, kungiyar ta bukaci a ba Musulmai hutun aiki a dukkan ranakun Juma’a kamar yadda yake a ranakun Asabar da Lahadi
  • Najeriya na da yawan Musulmai, amma duk da haka bas a more wasu hutu kamar yadda sauran addinai ke more a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Kungiyar kare haƙƙin Musulmi a Najeriya MURIC, ta buƙaci a yi wa kundin tsarin mulki gyara domin kafa kotunan Shari’a a dukkan jihohin Kudu maso Yamma na ƙasar nan.

Haka kuma, ƙungiyar ta nemi a ayyana Juma’a a matsayin hutun aiki na musamman ga Musulmai, domin sauƙaƙa musu wajen gudanar da ibada.

Wannan ƙira na daga cikin abubuwan da daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya gabatar yayin sauraron ra’ayoyin jama’a a zaman jin ra’ayi na yankin Kudu maso Yamma da Majalisar Dattawa ta shirya domin gyaran tsarin mulkin 1999.

An nemi a ba musulmai hutu ranar Juma'a
Ana nemawa Musulmai hutun aiki a ranakun Juma'a | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Abin da yasa MURIC ta dago maganar

Farfesa Akintola, Dr Jamiu Busari ya wakilta a taron, ya bayyana cewa babu ko guda daga cikin jihohin Kudu maso Yamma da ke da kotun Shari’a, duk da cewa akwai Musulmi da dama a yankin, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Wannan ya saba da yadda ake gudanar da shari’a a yankin Yarbawa Musulmi kafin zuwan Turawa. Yana nuna wariya ga Musulmai a tsarin shari’ar ƙasa.”

MURIC ta ce a samar da kotunan Shari’a a jihohin Kudu maso Yamma da suka haɗa da Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ondo, Ekiti da har da jihar Edo, domin magance ƙorafin Musulmai da kuma tabbatar da adalci.

A cewarsa, wadannan kotuna za su duba al’amuran Musulmai ne kawai, ba za su shafi Kiristoci ko sauran mutane ba.

A ayyana juma’a ranar hutu

Haka kuma, Farfesa Akintola ya buƙaci Majalisar Tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin hutu na kasa domin bai wa Musulmai damar gudanar da sallar Juma’a cikin kwanciyar hankali.

A cewarsa:

“A da, Musulmai suna amfani da Alhamis da Juma’a a matsayin hutun karshen mako. Amma yau, an mayar da Asabar da Lahadi wanda duk suka fi dacewa da bukatun Kiristoci.”

Ya ce wannan tsarin ya samo asali ne daga lokacin mulkin mallaka, inda aka fara bai wa Asabar rabin yini kafin daga baya a mayar da ita cikakken hutu a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon domin Mabiya cocin Seventh Day Adventist.

MURIC ta ce ana nuna wariya a hutu da bukukuwan ƙasa, inda ake da hutu guda 5 na Kiristoci (Kamar Kirsimeti, Sabon Shekara, Good Friday, Easter da Boxing Day) amma Musulmai na da uku kawai — Sallah Karama, Sallah Babba da Maulidi.

Ya kara da cewa:

“Muna rokon a duba yiwuwar ayyana Sabuwar Shekarar Musulunci a matsayin hutu na ƙasa.”

A amince da auren Islama a hukumance

Ya kuma nemi a amince da takardar shaidar auren Islama a matsayin shaidar aure mai karfi kamar yadda ake yi wa na coci ko auren kotu.

A cewarsa:

“Auren Kiristoci ana amincewa da shi a hukumance, amma na Musulmai ana ƙin amincewa da shi a wasu lokutan. Wannan cin zarafi ne.”

Ƙungiyar Musulmai ta yankin Kudu maso Yamma (MUSWEN) ma ta goyi bayan ƙiran kafa kotunan Shari’a da na tattalin arzikin Musulunci.

Sanata Opeyemi Bamidele, wanda ya wakilci Mataimakin Shugaban Majalisa, Sanata Jubrin Barau, ya tabbatar da cewa Majalisar Dattawa za ta duba dukkanin buƙatun da aka gabatar.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya ya ruwaito cewa, kungiyoyi da dama ciki har da na matasa, dalibai da mata sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.