Katsina: Yadda yara suka dauki bam a matsayin kayan gwangwan

Katsina: Yadda yara suka dauki bam a matsayin kayan gwangwan

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da samun labarin mutuwar cikon mutum na bakwai cikin yaran da bam ya tashi da su a cikin wata gona a kauyen 'Yanmama da ke karamar hukumar Malumfashi.

Hadimin Gwamna Aminu Masari na musamman, Muhammadu Garba ya bayyana cewa a tashin farko yara shida ne suka rasa rayukansu, sai kuma wacce a yanzu suka samu labarin mutuwarta, BBC Hausa ta ruwaito.

Ya ce: “Za a dauko ta yanzu a hada da sauran mutum shidan domin yi musu jana’iza. Akwai kusan akalla guda biyar da ke asibiti ana kula da su.”

Wannan shine karo na farko da aka samu irin haka a jihar, wacce ke mai fama da hare-haren 'yan fashin daji, inda hakan ya kara tsananta fargaba a zukatan al’umma.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce tuni aka tura masana a kan harkar abubuwa masu fashewa domin su gudanar da bincike game da wannan lamari.

Har ila yau hadimin gwamnan ya bayyana cewa yaran da abin ya faru da su, sun je gonar ne domin yin ciyawa.

Katsina: Yadda yara suka dauki bam a matsayin kayan gwangwan
Katsina: Yadda yara suka dauki bam a matsayin kayan gwangwan Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Sai suka tsinci wani abu mai nauyi, sun dauke shi da niyar za su bude shi, su ga ko mene ne", in ji shi.

Ya ce wasu daga cikin yaran sun ja hankalin sauran abokansu cewa abin da suka tsinta "bam ne". Yayin da sauran suka ce ba bam ba ne.

Zuwa yanzu dai hukumomi ba su sanar da ainahin ko menene abun da ya fashen ba, sannan kuma babu tabbaci kan yadda abun ya isa wannan gona.

Ya bayyana cewa matar da ke cikin gonar tare da yaran da suka tsinci bam din ta tabbatar wa jami'an tsaro cewa lallai abin da suka gani ya fi kama da gurnetin da aka nuna mata.

Ya ce: "jami'an tsaro sun kawo nau'o'in abubuwan fashewa inda suka nuna mata ko za ta iya shaida mai kama da abin da ta gani a hannun yaran".

“Matar wadda Allah Ya kubutar tare da 'ya'yanta ta umarci 'yarta ne ta mayar wa yaran da suka fara tsintuwar, bayan sun dawo sun ce su fa suna son kayansu."

Uwar yaran da suka tsira, wacce aka boye sunanta, ta ce ita da kanta ta nuna tantama lokacin da wani cikin yaran da suke tare ya ce ba shakka abin da suka tsinta "bam ne".

"Cikin gonar Alhaji Usaini, sai dan babban cikinsu ya ce bam ne. Ni kuma sai na ce kai! Wanne irin bam, a cikin gona" in ji ta.

Ta ce har sun mayar sun ajiye, su ma wadancan yaran sun kama hanya sun tafi, sai karamin danta ya nemi izini ta bar shi ya dauka don kuwa kayan gwangwan ne.

KU KARANTA KUMA: Magu: An ci moriyar ganga, an yada ta - Galadima

"Sai na ce dan Allah wannan ba bam ba ne. Kila cikin motocin nan da ke wucewa ne wani abu ya fita. Kila waya ce ciki. Sai ya ce to zai dauka ya kai wa mai gwangwan".

“Wadancan yaran na jin haka sai suka dawo suka ce su ne suka tsinta a ba su abinsu,” in ji matar.

A cewarta sun kama hanya ita da 'ya'yanta sun yi nisa, sai suka ji karar abin da ya fashe.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Gambo Isa ya ce yaro biyar a take suka rasu bayan fashewar.

Ya ce jami'ansu na can cikin gonar don ci gaba da bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng