Katsina: Fusatattun Matasa Sun Kai Hari kan Jami'an Hisbah, an Garzaya da Su Asibiti

Katsina: Fusatattun Matasa Sun Kai Hari kan Jami'an Hisbah, an Garzaya da Su Asibiti

  • Matasa sun kai hari ofishin Hisbah a Tandama, karamar hukumar Danja ta jihar Katsina, bayan sabani da jami’an
  • Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:10 na yamma, 13 ga Yuni, inda matasan suka fusata da tsawatarwar da jami’an Hisbah suka musu
  • Wasu daga cikin jami’an Hisbah sun jikkata, an garzaya da su asibitin Danja, ana bincike domin gano wadanda suka aikata harin da daukar mataki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Wasu matasa sun kuma kai hari kan jami'an hukumar Hisbah a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Matasan a unguwar Tandama da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina sun kai hari ofishin Hisbah bayan sabani kan askin kansu.

Matasa sun kai wa jami'an Hisbah hari
Wasu matasa sun kai hari kan jami'an Hisbah a Katsina. Hoto: Katsina State Hisbah Command.
Asali: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:10 na yamma ranar 13 ga Yunin 2025 da ke muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Katsina: Yadda hukumar Hisbah ke fama da matasa

Hukumar Hisbah na fuskantar matsaloli daga wasu matasa yayin da suke yawan kai musu farmaki kan saba abin da suke yi.

A kwanakin baya, matasa sun jikkata jami'an hukumar Hisbah bayan hana su buga kwallo kusa da masallaci.

Rundunar ‘yan sanda ta cafke Alhaji Surajo Mai Asharalle da wasu uku kan zarginsu da kai wa jami’an Hisbah hari, inda suka jikkata su.

Hisbah ta ce jami’anta sun je dakatar da matasa daga wasan ƙwallo kusa da masallaci, amma sai matasan suka bijire, suka kore su.

A lokacin arangamar, Surajo Mai Asharalle ya harba bindiga sau da yawa, inda ya jikkata jami’an Hisbah biyar da ke bakin aiki.

An sake kai hari kan jami'an Hisbah a Katsina
Wasu fusatattun matasa sun jikkata jami'an Hisbah a Katsina. Hoto: Legit.
Asali: Original

Matasa sun farmaki jami'an Hisbah a Katsina

Hakan ya biyo bayan tarwatsa wasu matasa da jami'an suka yi kan gyaran gashinsu, lamarin da ya rikide zuwa fada.

Matasan sun farmaki ofishin Hisbah, inda suka jikkata wasu jami’ain hukumar da dama kan sabanin da aka samu.

Wasu da dama sun samu raunuka yayin da aka garzaya da su asibitin garin Danja domin samun kulawar gaggawa

Rundunar ‘yan sanda ta ce suna gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan hari da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

Lamarin ya jawo cece-kuce kan yadda jami’an Hisbah ke wuce gona da iri da sunan kula da tarbiyya, suna tauye ‘yancin jama’a.

Wasu mutane sun nuna rashin jin dadi da yadda Hisbah ke tsoma baki a rayuwar mutane, abin da ke haddasa rikici a cikin al’umma.

Hisbah ta kwace kalaban giya a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta samu nasarar ƙwace barasar da aka yi niyyar shigar da ita zuwa ƙaramar hukumar Daura.

Hukumar ta ƙwace barasar wacce ta kai kimanin katan 142 a yayin wani aikin sintiri domin kawar da munanan ɗabiu da rashin ɗa'a.

Hisbah ta kuma sake gurfanar da wasu ƴan mata guda biyu a gaban kuliya bayan sun ƙi ɗaukar shawarwari da nasihohin da aka yi musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.