Jigon APC da Ya Taba Gargadin Bola Tinubu kan Zaben 2027 Ya Rasu

Jigon APC da Ya Taba Gargadin Bola Tinubu kan Zaben 2027 Ya Rasu

  • Babban jigon jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma lauya mai sharhi kan siyasa, Jesutega Onokpasa, ya riga mu gidan gaskiya
  • Onokpasa ya taka rawa a matsayin mamba a kwamitin yaɗa labarai da kuma kwamitin kamfen na shugaban kasa a zaɓen 2023
  • Ya bar mata da ‘ya’ya, kuma har yanzu ba a bayyana dalilin mutuwarsa ba, lamarin da ya girgiza dandalin siyasa a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da rasuwar sanannen lauya kuma mai ruwa da tsaki a harkar siyasa kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan APC a Najeriya, Jesutega Onokpasa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu ba a tabbatar da dalilin rasuwar Jesutega Onokpasa ba a hukumance.

Jigon APC, Jesutega Onokpasa ya rasu
Kusa a APC, Jesutega Onokpasa ya rasu. Hoto: @Onsogbu
Asali: Twitter

Wani masoyin jam’iyyar APC kuma ɗan fafutukar goyon bayan gwamnatin Tinubu, Okezie Atani, ne ya sanar da rasuwar Onokpasa a shafinsa na X a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okezie Atani ya rubuta cewa:

“Mun rasa Barista Jesutega Onokpasa.”

An yi jimamin jagora a APC da rasu

Onokpasa ya kasance sananne a fagen siyasa da sharhi kan harkokin mulki, inda ya rika bayyana ra’ayinsa kai tsaye kan manufofi da matsalolin gwamnati.

A lokacin zaɓen shugaban kasa na 2023, ya taka muhimmiyar rawa a matsayin mamba na Kwamitin Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC da kuma Kwamitin Kamfen na Shugaban Kasa.

Shafin Facebook na Renewed Hope United Kingdom ya wallafa takaitaccen sakon ta'aziyya mai taken 'bankwana da mai kishin kasa.'

A cikin sakon, an bayyana cewa mutuwar Jesutega Onokpasa babban rashi ne ga Najeriya baki daya.

Yadda jigon na APC ya gargadi Tinubu kan 2027

A watan Disambar 2024, Onokpasa ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda Shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da mulki, inda ya ce zai iya daina marawa shugaban baya a zaben 2027.

A kalamansa da tashar Arise News ta wallafa a X, Jesutega Onokpasa ya ce:

“Ba zan goyi bayan Shugaba Tinubu a 2027 ba idan bai dawo daga hanyar da ya dauka ba.
"Dole ne ya girmama ‘yan jam’iyyar da suka tsaya masa, maimakon bai wa wadanda suka raina mu mukamai.”

Wannan furuci ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar, kasancewar Onokpasa yana daga cikin fitattun ‘yan jam’iyyar da suka bayyana goyon bayansu tun farko ga Tinubu.

Wasu 'yan APC sun yi alhini da cewa:

“Muryarsa, ko da tana goyon baya ko suka, ta kasance muhimmiya a tattaunawar dimokuradiyya a Najeriya. Zai yi wahala a manta da shi.”
'Yan APC sun yi jimamin rasuwar jigon jam'iyyar
'Yan APC sun yi jimamin rasuwar jigon jam'iyyar da ya rasu. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya, kuma ana fatan Allah ya ba su juriyar jure wannan babban rashin da suka yi.

APC ta gargadi Ndume kan sukar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta gargadi Sanata Ali Ndume kan sukan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ali Ndume ya yi magana ne kan yadda 'ya siyasa ke sauya sheka suna marawa Bola Tinubu baya a Najeriya.

Sakataren yada labaran APC, Bala Ibrahim ya bayyana cewa suna girmama Ali Ndume amma hakan bai ba shi damar munana kalamai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng