Gwamna Zulum Ya Tuna da Iyalan Sojojin da Suka Rasu a Fagen Daga, Ya ba Su Tallafi

Gwamna Zulum Ya Tuna da Iyalan Sojojin da Suka Rasu a Fagen Daga, Ya ba Su Tallafi

  • Gwamna jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba da tallafi ga iyalan sojojin da suka rasu a fagen daga
  • Zulum ya ba da gudunmawar N100m domin rabawa iyalan sojojin da suka rasu da kuma sojojin da suka samu raunuka
  • Gwamna Zulum ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci ga ba aiki kafaɗa da kafaɗa tare da hukumomin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da gudummawar kuɗaɗe ga iyalan sojojin da suka rasu ko suka samu raunuka.

Gwamna Zulum ya ba da N100m domin tallafawa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka ji rauni a yaƙin da ake yi da ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Gwamna Zulum ya ba sojoji tallafi
Gwamna Zulum ya ba da tallafin N100m ga iyalan sojoji Hoto: Dauda Iliya
Asali: Facebook

Mai magana da yawun bakin Gwamna Zulum, Dauda Iliya ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayar da wannan tallafin ne a ranar Asabar yayin liyafar bikin babbar Sallah (Eid El-Kabir) da aka gudanar a Maiduguri

Babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, da babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, suka shirya liyafar a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Gwamna Zulum ya ba da tallafin kuɗi

Gwamna Zulum ya miƙa takardar cakin na N100m ga kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdussalam Abubakar.

Ya bayyana cewa kowane soja da ya ji rauni a filin daga zai samu N500,000, yayin da sauran kuɗin za a raba wa iyalan sojojin da suka rasu a yayin aikin.

An shaida miƙa cakin ne tare da halartar babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar da kwamandan rundunar hadin gwiwa ta MNJTF, Manjo Janar Godwin Mutkut.

Sauran manyan baƙi da suka halarta sun haɗa da ɗan Majalisar Wakilai, Injiniya Bukar Talba, Sakataren Gwamnatin Jihar Borno, Alhaji Bukar Tijjani, shugaban ma’aikata, Dr Muhammad Ghuluze.

Sauran sun haɗa da muƙaddashin Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Dr Babagana Mustapha Mallumbe, da shugaban jam’iyyar APC na jiha, Bello Ayuba, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

Gwamna Zulum ya yabawa sojoji

Gwamna Zulum ya yaba da jajircewa da ƙaunar ƙasa da dakarun Najeriya ke nunawa, inda ya jaddada cewa bai kamata a taɓa mantawa da sadaukarwarsu ba.

Gwamna Zulum ya yabawa sojoji
Gwamna Zulum ya yabawa jajircewar sojoji Hoto: Dauda Iliya
Asali: Facebook

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa rundunonin tsaro goyon baya.

"Jajircewarku a fagen fama, a cikin mawuyacin hali kuma nesa da iyalanku, ba ta ɓace mana ba. Muna godiya ƙwarai da gaske, ba za mu taɓa ɗaukar sadaukarwarku da wasa ba."
"Jihar Borno za ta ci gaba da zama tare da sojojin Najeriya da duka hukumomin tsaro a yaƙin da ake yi da ta’addanci da kuma sake gina al’umma domin samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa."

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Sojoji sun hallaƙa kwamandojin ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu kwamandojin ƙungiyar ISWAP.

Dakarun sojojin sun hallaka kwamandojin ne yayin wani artabu da suka yi da su a maɓoyarsu da ke cikin daji.

Kashe kwamandojin ya nuna irin gagarumar nasarar da dakarun sojoji suke samu a yaƙin da suke da ƴan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng