Bikin Sallah: Gwamna Ahmed Aliyu Ya Gwangwaje Ma'aikatan Jihar Sokoto

Bikin Sallah: Gwamna Ahmed Aliyu Ya Gwangwaje Ma'aikatan Jihar Sokoto

  • Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya tuna da ma'aikata yayin da aka tunkari bukukuwan babbar Sallah
  • Ahmed Aliyu ya umarci a biya ma'aikatan jihar albashinsu na watan Yuni da wuri don su yi bukukuwan Sallah cikin walwala
  • Gwamnan ya kuma buƙaci ma'aikatan da suka.ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu a faɗin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ba da umarnin biyan albashin watan Yuni da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati a faɗin jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ba da umarnin fara biyan albashin ne tun daga ranar Litinin, domin ba ma'aikata damar shiryawa bikin Sallah ta Layya (Eid-el-Kabir) da ke tafe.

Gwamna Ahmed Aliyu
Gwamnan Sokoto ya umarci a biya ma'aikata albashi Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

Wannan umarni na musamman ya fito ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamna, Malam Abubakar Bawa, ya fitar ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a biya ma'aikata albashi da wuri a Sokoto

Malam Abubakar Bawa ya bayyana cewa umarnin ya shafi ma’aikata a matakin jiha da na ƙananan hukumomi, ciki har da ma’aikatan hukumar ilmi ta ƙananan hukumomi (LGEA) da kuma ƴan fansho.

A cewarsa, wannan ne karo na uku da gwamnatin Ahmed Aliyu ke biyan albashi da wuri domin tallafawa ma’aikata a lokutan bukukuwa.

Gwamnan, wanda yanzu haka yake ƙasar Saudiyya domin aikin Hajji, ya ce wannan mataki na da nufin sauƙaƙa matsin tattalin arziƙi da ke kan ma’aikata tare da ba su damar siyan dabbobin layya da sauran shirye-shiryen bikin Sallah.

“Ina amfani da wannan dama na tunatar da ma’aikata karin maganar da ke cewa, Wanda aka kyautata masa ana sa ran zai rama biki."
“Saboda haka, ina sa ran ku dukkanku za ku nuna kishi da jajircewa a wuraren aikinku."

- Gwamna Ahmed Aliyu

Gwamnan Sokoto na kyautatawa ma'aikata

Ya bayyana wasu daga cikin shirin jin ƙai da gwamnatinsa ta aiwatar domin tallafa wa ma’aikata.

Cikin abubuwan har da biyan albashi a kan lokaci, dawo da ba da tsabar kuɗi ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati, rabon kayan Sallah, biyan bashin fansho da na giratuti da aka dade ana bin gwamnati.

Gwamna Ahmed Aliyu
Gwamna Aliyu ya bukaci ma'aikata su kara jajircewa Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter
“Ina sa ran ma’aikata za su mayar da martani ta hanyar zuwa aiki da wuri da kuma nuna nagarta a ayyukansu.”

- Gwamna Ahmed Aliyu

Gwamna Ahmed Aliyu ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na farfado da fannin ma’aikata domin samar da kyakkyawan shugabanci da nagartaccen aiki.

Ya kuma tabbatar wa da jama’ar jihar cewa gwamnati za ta ci gaba da raba romon dimokuradiyya a kowane yanki na jihar.

A ƙarshe, ya yi wa dukkan mazauna jihar fatan a yi bikin Sallah lafiya da annashuwa.

An taimakawa ma'aikata

Wani mazaunin Sokoto, Muhammad Dalhat, ya bayyana cewa matakin da gwamnan ya ɗauka zai taimakawa ma'aikata su yi bikin Sallah cikin walwala.

"Eh gaskiya ma'aikata za su ji daɗin hakan domin za su samu su yi bikin Sallah ba tare da wata tangarɗa ba."

"Wanda bai samu damar siyan ragon layya ba, sai ya garzaya kasuwa ya siya."

- Muhammad Dalhat

Gwamnan Sokoto ya yi magana kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya nuna damuwa kan rashin tsaro.

Gwamna Ahmed Aliyu ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar.

Ahmed Aliyu ya sanar da ɗaukar sababbin matakai don ganin cewa matsalar ƴan bindiga da ƴan ta'adda ta zo ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng