Dattawan Zamfara Sun Fallasa Gwamna Dauda kan Matsalar Rashin Tsaro
- Ƙungiyar dattawan Zamfara ta nuna rashin jin daɗinta dangane da halayen da Gwamna Dauda Lawal yake nunawa kan matsalae tsaro
- Dattawan sun zargi gwamnan da ƙoƙarin nuna cewa nasarorin da ake samu a fannin tsaro a Arewa maso Yamma, na samuwa ne ta dalilinsa
- Ƙungiyar ta nuna cewa hakan bai dace ba domin son zuciya ne da yunƙurin cimma wata manufa ta siyasa
- Hakazalika, ƙungiyar ta zargi Gwamna da kasa cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe na kawo ƙarshen rashin a wata ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƙungiyar dattawan Zamfara ta soki Gwamna Dauda Lawal saboda ƙoƙarin nuna cewa shi ne ya assasa nasarar da aka samu a fannin tsaro Arewa maso Yamma da kansa.
Ƙungiyar dattawan ta zargi gwamnan da yin siyasar son rai da kuma gazawa wajen cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensa.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Laraba, ta hannun sakataren ta, Alhaji Umaru Yusuf Tsafe, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattawan Zamfara sun taso Gwamna Dauda a gaba
Ƙungiyar ta bayyana cewa abin da gwamnan yake yi bai dace ba kuma son zuciya ne.
Dattawan sun zargi Gwamna Dauda Lawal da kasa cika alƙawarin da ya yi a lokacin zaɓen 2023 cewa zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar Zamfara cikin wata guda.
Ƙungiyar ta ce bayan ya kasa cika alƙawarin sai ya koma yana ɗora laifi kan gwamnatin tarayya lokacin da matsalar tsaron ta ƙara ta'azzara a ƙarƙashin mulkinsa.
Sun bayyana cewa a lokacin yaƙin neman zaɓe, Gwamna Dauda Lawal ya riƙa zargin Bello Matawalle da haifar da rashin tsaro a Zamfara.
“Gwamna Dauda Lawal ya hau kujerar mulki ne bisa dogaro da alƙawuran da ya kasa cikawa."
"Yana hawa mulki, sai ya ce bai da kayan aikin da za su ba shi damar ɗaukar mataki, hakan ya bayyana ƙarancin hangen nesa da kwarewa a shugabanci.”
- Alhaji Umaru Yusuf Tsafe
Wane zargi aka yi kan Gwamna Dauda?

Asali: Twitter
Dattawan sun zargi Gwamna Dauda da ƙoƙarin karɓe nasarorin tsaro da aka samu cikin kwanakin nan.
Sun bayyana cewa nasarorin da aka samu ƙoƙari ne na Shugaba Bola Tinubu, Malam Nuhu Ribadu, Dr. Bello Muhammad Matawalle, da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa.
Gwamna Dauda ya faɗi halin da ya tarar da Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya koka kan halin da ya tarar da jihar bayan mulkin tsohon gwamna Bello Matawalle.
Dauda Lawal ya bayyana cewa N4m kawai Bello Matawalle ya bar masa a asusun jihar sai kuma ɗumbin basussuka.
Gwamna Dauda ya bayyana cewa ya gaji basussuka da yawa na albashin ma'aikata da aka daɗe ba a biya su ba.
Ya ƙara da cewa da hawansa kan mulki, ya ɗauki matakan ganin cewa ya warware tarin matsalolin da ya tarar da jihar a ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng