Jonathan Ya Yi Hasashen Nasarar Tinubu a Zaben 2027? An Gano Gaskiya

Jonathan Ya Yi Hasashen Nasarar Tinubu a Zaben 2027? An Gano Gaskiya

  • Wasu rahotanni sun yaɗu a shafukan sada zumunta waɗanda suka danganta Goodluck Jonathan da yin magana kan zaɓen shugaban ƙasa
  • Rahotannin sun yi iƙirarin cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaɓen 2027
  • An gudanar da bincike domin gano sahihancin waɗannnan rahotanni waɗanda suka yaɗu a shafukan sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An yaɗa wani rahoto da ke iƙirarin cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi hasashen nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Rahoton hasashen tsohon shugaban ƙasan kan nasarar Bola Tinubu a 2027, an fara yaɗa shi ne a ranar Talata, sannan ya karaɗe shafukan sada zumunta.

Goodluck Jonathan da Bola Tinubu
Jonathan bai yi hasashen nasarar Tinubu a zaben 2027 ba Hoto: Goodluck Jonathan, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar TheCable ta yi bincike domin gano sahihancin labarin wanda aka yaɗa a shafukan sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yaɗa cewa Jonathan ya hango nasarar Tinubu

Taken rahoton ya ce:

"Tinubu zai ci zaɓen shugaban ƙasa na 2027 - Goodluck Jonathan."

Ana zargin cewa jaridar Daily Post ce ta wallafa wannan rahoto a ranar 15 ga watan Afrilu, 2025.

An yaɗa rahoton sosai a shafukan Facebook da dama masu tarin mabiya, haka kuma ya samu karɓuwa sosai a TikTok.

Za a iya samun rahoton a nan da nan.

An gudanar da bincike kan lamarin

Jaridar wadda aka danganta da rahoton da ke yawo, ba ta wallafa wani labari makamancin haka ba.

Bincike a shafinta da labaran da ta wallafa bai nuna wani abu da ya shafi cewa tsohon shugaban ƙasan ya yi irin wannan hasashen ba.

Haka kuma, tambarin da ke yawo ya bambanta da na asalin jaridar dangane da girma da irin rubutun da aka yi amfani da shi, abin da ke nuna cewa hoton na ƙarya ne.

Bugu da ƙari, babu wata sahihiyar kafar yaɗa labarai da ta ruwaito cewa Jonathan ya furta irin wannan magana.

Goodluck Jonathan da Bola Tinubu
An yi bincike kan ikirarin cewa Jonathan ya hango nasarar Tinubu a 2027 Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

An ji ta bakin hadiman Hadiman Jonathan

An kuma tuntubi tawagar yaɗa labarai ta Jonathan don tabbatar da sahihancin rahoton.

Mataimaki na musamman ga tsohon shugaban ƙasan, Ikechukwu Eze, ya ƙaryata iƙirarin.

Ikechukwu Eze ya bayyana rahoton a matsayin labarin da ba gaskiya a ciki wanda wakilan yaɗa ƙarya suka ƙirƙira.

"Babu wani lokaci da Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana da kowanne ɗan jarida kan zaɓen 2027 da ke tafe."

- Ikechukwu Eze

Abin da bincike ya nuna

Iƙirarin cewa Goodluck Jonathan ya yi hasashen nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ƙarya ne.

Zuwa yanzu babu inda Tinubu ya fito ya shaidawa duniya cewa zai nemi a sake ba shi kuri'u idan an shirya zabe.

Jonathan ya magantu kan dakatar da Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yi magana kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers.

Jonathan ya bayyana cewa dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara abu ne wanda zai ɓata sunan Najeriya a idon ƙasashen duniya.

Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa ko kaɗan bai dace ba a ɗauki matakin da dakatar da shugabannin da aka zaɓa daga kan muƙamansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng