'Ku Zo da Shaida': Saƙon Iyalan Idris Dutsen Tanshi ga Wasu da Suka Sayi Filayensa
- An bukaci duk wanda ya sayi fili daga marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi ya hallara a filin a ranakun Asabar da Lahadi masu zuwa
- Wannan kira ya zo ne da bukatar masu filaye su zo da shaidunsu da takardun saye domin duba sahihancin mallaka ko wasu dalilai
- Babu cikakken bayani kan dalilin hakan, amma wasu na ganin yana da nasaba da rasuwar marigayin da ke neman fitar da hakkin al'umma
- Hakan ya biyo bayan rasuwar marigayin wanda ya ba da gudunmawa sosai a rayuwarsa wurin koyar da al'ummar Musulmi addini
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Iyalan marigayi Malam Idris Dutsen Tanshi sun fitar da sanarwa kan filayensa a jihar Bauchi .
Iyalan sun bukaci cewa duk wanda ya san ya sayi fili a bayan 'Mobile Barrack' ya hallara a filin da shaidasa.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi ya wallafa a manhajar Facebook a yau Alhamis 17 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehi ya yabawa ɗaliban Idris Dutsen Tanshi
Legit Hausa ta ruwaito cewa wani malamin Musulunci ya yaba da jajircewar daliban marigayi Malam Idris Dutsen Tanshi kan wasiyyar da ya bari.
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya jinjinawa daliban marigayi Dutsen Tanshi bisa mutunta wasiyyar da malamin ya bar musu kafin rasuwarsa.
Sheikh Ibrahim ya ce abin yabawa ne ganin yadda daliban suka tsaya kan wasiyyar malaminsu inda ya ce har a tsaye ake karɓar gaisuwar ta'aziyya.
Malamin ya bayyana cewa bai samu halartar jana'izar ba saboda cunkoson al'umma, amma ya yi masa addu'a Allah ya gafarta masa da kuma biya shi da gidan aljanna.

Asali: Twitter
Sakon daliban marigayi Dutsen Tanshi ga al'umma
A cikin sanarwar, an bukaci al'umma su zo a ranakun Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna shaidarsu.
A cewar sanarwar:
“Duk wanda yasan ya sayi fili a wajen Dr. Idris a filayensa na bayan 'MOBILE BARRACK' ya zo a ranar Asabar da Lahadi da shaida, a filin.”
Sanarwar ta bukaci masu filayen su zo da takardunsu da kuma shaidu domin tantance wa bayan ya sayar musu da filin a yankin.
Ko da yake ba a bayyana dalilin hakan ba, wasu na ganin bai rasa nasaba da tabbatar da cire hakkin mamacin.
An sake gargadin masu ta'azziyar Dutsen Tanshi
A baya, kun ji cewa dalibai marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi sun sake fitar da sanarwa, suna jan hankalin al'umma kan wasiyyar da aka bari.
Daliban sun gargadi jama’a da su guji daukar hotuna ko bidiyo a wurin ta'aziyya sannan su daina yadawa a kafafen sada zumunta na zamani.
Sun bayyana cewa Sheikh Dutsen Tanshi tun yana raye yana Allah-wadai da masu yada hotonsa ko bidiyo a kafafen sadarwa ba tare da izini ba.
A cikin sanarwar da aka wallafa a Facebook, sun sake nanata cewa ba a yarda da daukar hoto ko bidiyo wajen ta’aziyya ba, suka bukaci a kiyaye.
Asali: Legit.ng