Dokar Batanci: Izala Ta Fadi Matsayarta bayan Hukuncin Kotun ECOWAS
- Kungiyar JIBWIS ta bayyana rashin amincewarta da umarnin kotun ECOWAS na gyara dokar batanci ga fiyayyen halitta
- JIBWIS ta jaddada cewa dokar batanci da aka samar a jihar Kano tana da tushe har a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya
- Ta ce sassa na 38(1) da 4(7) suna bai wa jihohi damar samar da dokoki bisa addini da al’ada, don haka dokar tana kan turba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta mayar da martani kan hukuncin da kotun ECOWAS ta yanke, wanda ya umarci gwamnatin tarayya da ta yi wa dokar batanci ta jihar Kano gyaran fuska.
JIBWIS, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ta bayyana matuƙar damuwa da wannan hukunci da kotun ta ECOWAS ta yanke a ranar 9 ga Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan
"Sai yanzu ka san yana da kima?" El Rufa'i ya tunawa Ganduje ya kira Buhari Habu na Habu

Asali: Facebook
A saƙon da Sheikh Abdullahi Bala Lau ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ba za su amince da hukuncin kotun ba, wanda ke buƙatar gwamnati ta soke ko ta gyara sassa na 210 da 382(b) na dokokin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
JIBWIS ta bayyana cewa hukuncin kotun karan-tsaye ne kai tsaye ga tsarkin addinin Musulunci, musamman a jihar Kano, inda kashi 99 cikin 100 na al’umma Musulmai ne.
Kungiyar Izala ta soki hukuncin kotun ECOWAS
A cikin sanarwar da JIBWIS ta fitar, kungiyar ta jaddada cewa sashe na 38(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayar da haƙƙin walwala da bin addini.
Sanarwar ta ce:
“Wannan ya haɗa da ‘yancin aiwatar da dokokin addini bisa abin da mutum ya yi imani da shi. Bugu da ƙari, sashe na 4(7) na kundin tsarin mulki ya bai wa majalisun dokoki na jihohi damar tsara dokoki kan al’amuran da suka shafi laifuka.”
“Don haka, ƙirƙirar dokar shari’ar Musulunci ta jihar Kano da sashe na 382(b) ya yi daidai da kundin tsarin mulki, kuma ya dace da haƙƙin ƙirƙirar dokokin da suka yi daidai da al’ada da addini.”
JIBWIS: “Inda hukuncin batanci ya samo asali”
Sanarwar da shugaban JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, da Sakataren kungiyar, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, suka sa wa hannu, ta ce hukuncin batanci ya samo asali ne daga Al-Kur’ani.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Sashe na 382(b) na dokar shari’ar Musulunci, wanda ke hukunta wanda ya zagi ko ya ɓata suna ga Annabi Muhammad (SAW) da hukuncin kisa, ya samo asali ne daga Alƙur’ani mai girma da sunnonin Annabi (SAW).”
“Kare mutuncin Annabi Muhammad (SAW) wani ɓangare ne da ba za a taɓa sassauci da shi ba a cikin addinin Musulunci. Zagin Annabi ba ‘yancin faɗar albarkacin baki ba ne — babban laifi ne da ke barazana ga zaman lafiya da ɗorewar dangantakar addinai.”
Martanin gwamnatin Kano ga hukuncin ECOWAS
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta fadi matsayinta kan hukuncin da kotun ECOWAS ta yanke dangane da dokar batanci, tana mai cewa tana da ikon kare tsarkin addini jama'arta.
A wata sanarwa da ya fitar, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Garba Waiya, ya bayyana cewa jihar ba za ta ja da baya kan dokar da ta tanadar don dakile kalaman batanci ba.
A ranar 9 ga Afrilu, 2025, ta yanke hukunci cewa wasu sassa na dokokin jihar Kano da suka shafi batanci sun saba wa ka’idojin kare haƙƙin ɗan Adam, lamarin da musulmi suka yi fatali da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng