An Rage Mugun Iri: Ɗan Bindiga Ya Sheƙa Lahira bayan Kamuwa da Cutar Farfaɗiya

An Rage Mugun Iri: Ɗan Bindiga Ya Sheƙa Lahira bayan Kamuwa da Cutar Farfaɗiya

  • Wani da ake zargi ya na cikin masu garkuwa da mutane, Chumo Alhaji daga Babanla, ya mutu bayan ya kamu da ciwon farfadiya a Kwara
  • Rahotanni sun ce an kama Chumo Alhaji kan zargin shirya sace Shehu Garba, Sreiki Fulani na Ajase Ipo da wani dan kasuwa mai suna Ali Garba
  • Alhaji ya fara jin ciwon farfadiya a hannun ’yan sanda, sai aka garzaya da shi asibitin rundunar, a nan aka ba shi kulawa sannan aka sallame shi
  • Washegari sai ciwon ya dawo, aka kai shi asibiti, amma duk da kokarin likitoci, ya rasu, an tura gawarsa zuwa asibitin koyarwan Oke Oyi ayi bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Wani da ake zargi ya na cikin masu garkuwa da mutane ne ya yi mutuwar wulakanci a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan kisan ɗan bindiga, miyagu sun ɗauki fansa, sun ƙona masallacin Juma'a

Ɗan bindigar mai suna Chumo Alhaji daga Babanla, ya rasu bayan ya sha fama da ciwon farfadiya a asibitin yan sanda.

Dan bindiga ya yi wani irin mutuwa a hannun yan sanda
Dan bindiga ya mutu a hannun yan sanda bayan ya kamu da cutar farfaɗiya. Hoto: Legit.
Asali: Original

Majiyoyi sun shaidawa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne a ranar 12 ga Afrilu, 2025, da karfe 10 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dan bindiga ya yi mutuwar wulakanci

A baya, rahoton Legit Hausa ya kawo muku cewa wani 'dan bindiga, Kachalla Dan Lukuti, ya rasu bayan fama da wata muguwar cuta da ta sa ya fara yin haushin kare.

Majiyoyi sun ce ya kamu da wannan cuta mai ban mamaki mako daya da ya gabata, inda ya fara kukan kare kafin ya mutu.

Mutanensa sun tsorata da halin da ya shiga, sun tilasta wa mazauna garin Kizara su yi masa jana'iza a makarantar firamare.

Kwara: Cutar farfaɗiya ta kama ɗan bindiga

An kama Alhaji bisa zargin shirin sace fitattun mutane a Ajase Ipo ciki har da Shehu Garba, Sreiki Fulani na Ajase Ipo da wani dan kasuwa, Alhaji Ali Garba.

Kara karanta wannan

Yadda darektan APC ya yi wani irin mutuwa a hannun ƴan bindiga a Abuja

Marigayin ya fara jin alamar farfadiya, aka garzaya da shi asibitin ’yan sanda domin ceto rayuwarsa.

An fara tunanin kamar ciwon farfadiya ne, daga baya aka sallame shi daga asibitin domin komawa hannun yan sanda.

Dan bindiga ya mutu a hannun yan sanda
Cutar farfaɗiya ta yi ajalin dan bindiga a Kwara. Hoto: Kwara State Police Command.
Asali: Facebook

Farfaɗiya ta hallaka ɗan bindiga a Kwara

Washegari, ranar 13 ga Afrilu, Alhaji ya sake kamuwa da ciwon farfadiya, aka dawo da shi asibiti domin karin kulawa.

Sai dai duk da kulawar da aka ba shi, Alhaji ya rasu nan take a asibitin bayan lamarin ya mununa.

Tuni aka tura gawarsa zuwa asibitin koyarwa na Oke Oyi domin a gudanar da binciken likitoci.

Zamfara: Yan bindiga sun kona masallacin Juma'a

A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kona masallacin Juma’a, asibitin kula da lafiya da gidaje fiye da goma a Biyabiki, Zamfara.

Hare-haren sun faru ne da misalin karfe 8 na dare a ranar Laraba 12 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ramuwar gayya kan kisan 'yan uwan Ado Aliero.

Shaidu sun ce ba a yi garkuwa ko kisa ba, amma 'yan bindigar sun kona gine-gine sannan suka tsere bayan kusan awa guda suna barna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel