Ana Batun Dakatar da Fubara, Masu Zanga Zanga Sun Mamaye Ofishin Gwamna, an Ji Dalili
- Masu zanga-zanga sun fusata kan kisan kiyashin da ƴan bindiga suke yi musu a jihar Ondo da ke yankin Kudancin Najeriya
- Fusatattun masu zanga-zangar sun mamaye gidan gwamnatin jihar Ondo da sanyin safiyar ranar Laraba, 19 ga watan Maris 2025
- Mutanen dai sun je gidan gwamnatin ne domin nuna adawarsu kan kisan da ƴsn ɓindiga suka yi wa manoma a ƙaramar hukumar Akure ta Arewa
- Fusatattun mutanen sun koka da nuna halin ko in kula da gwamnatin jihar ke nunawa kan ta'asar da ƴan bindiga suke yi musu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Fusatattun masu zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnatin jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yamma na Najeriya.
Fusatattun masu zanga-zangar sun rufe ofishin gwamna da ke Alagbaka, Akure, babban birnin jihar, Ondo.

Asali: Twitter
Jaridar Leadership ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun ɗauki matakin ne saboda kisan wasu manoma biyar da ƴan bindiga suka yi a ƙauyen Aba Oyinbo da ke ƙaramar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa an harbe manoman ne a wani sabon hari da ƴan bindigan suka kai da sanyin safiyar ranar Laraba, 19 ga watan Maris 2025.
Masu zanga-zanga sun soki gwamnati
Masu zanga-zangar sun fusata da yadda gwamnatin jihar ke nuna halin ko-in-kula kan yawaitar kashe-kashen.
Fusatattun mutanen sun kutsa cikin ofishin gwamna, suka ajiye gawarwakin mutanen da aka kashe domin nuna rashin jin dadinsu.
Fasinjoji da direbobi da ke kan titin Akure/Owo sun maƙale yayin da masu zanga-zangar suka taru a Ogbese, inda suka toshe hanyar domin nuna rashin amincewa da halin da ake ciki.
Idan ba a manta ba, kimanin makonni biyu da suka gabata, ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe manoma 20 a gidajen gona huɗu da ke cikin wannan ƙaramar hukuma.
Ayyuka sun tsaya a ofishin gwamna Ondo
An dakatar da ayyuka a ofishin gwamnan jihar har na tsawon sa’o’i sakamakon zanga-zangar.
Zanga-zangar zuwa ofishin gwamna ita ce ta biyu a cikin makonni kaɗan da suka gabata bayan ƙaruwar sace-sacen mutane a jihar.
Masu zanga-zangar sun rufe ofishin gwamna saboda yawaitar sace-sacen mutane da kuma gazawar hukumomin tsaro wajen daƙile ayyukan ƴan bindiga.
Sun nuna damuwa cewa ƴan ta’adda na cin karensu babu babbaka duk da ƙoƙarin jami’an tsaro.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an kashe manoman ne da safiyar Laraba, ta hannun wasu da ake zargin makiyaya ne.
Wasu manoma ma sun toshe hanyar Akure/Owo, suna zanga-zanga kan sace-sace da kashe-kashen da ake yi a yankin.
Mutane sun yi zanga-zanga a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu masu zanga-zanga sun mamaye tituna a Abuja sakamakon rikicin zaɓen ƙanananan hukumomin jihar Benue.
Masu zanga-zangar sun fito ne domin nuna adawarsu da matakin da aka ɗauka na maida zaman kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƙananan hukumomin jihar Benue zuwa birnin Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng