"Sauƙi daga Allah": Ana tsakiyar Azumi, Farashin Kayayyaki Sun Ƙara Sauka a Najeriya
- Hukumar NBS ta bayyana cewa an sake samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a watan Fabrairun 2025
- A cewar hukumar, alkaluman hauhawar farashin ya yi ƙasa zuwa kashi 23.18% a watan Fabrairu, ƙasa da 24.48% na watan Janairu
- Hukumar ta bayyana cewa farashin kayan abinci ya sauka a birane da karkara idan aka kwatanta da yadda ya hauhawa a bara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 23.18% a watan Fabrairu 2025.
Hukumar NBS ta tabbatar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya sake yo ƙasa karo na biyu kenan bayan raguwar da ya yi a watan Janairu.

Asali: Getty Images
NBS ta ce wannan sauƙin da ake samu ya biyo bayan sabunta ma'aunin hauhawar farashin watau CPI, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
2027: Matasa sun kaucewa tafiyar El Rufai a SDP, sun kama Peter Obi da Gwamna Bala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda farashin kaya ya karye a Najeriya
A watan Disamba 2024, alƙaluman hauhawar farashi ya kai kashi 34.80%, amma bayan sake fasalin ma'aunin CPI da sabunta shekara zuwa 2024 maimakon 2009, an ga sauyi mai girma.
Gagarumin sauyin da aka samu wajen tantance alƙaluman kididdiga ya sanya hauhawar farashi raguwa zuwa kashi 24.48% a a watan Janairu, 2025.
Hauhawar farashin abinci ya ragu
A bangaren kayayyakin abinci, NBS ta ce hauhawar farashin abinci a Fabrairu ya tsaya a ragu zuwa 23.51% idan aka kwatanta da kashi 37.92% da aka samu a Fabrairu 2024.
Amma idan aka duba alƙaluman wata zuwa wata, hauhawar farashin kayan abinci ya dawo kaso 1.67% a qatan Fabrairu 2025..
Abinci ya sauka a biranen Najeriya
A birane, hauhawar farashi a watan Fabrairu ya kasance 25.15% idan aka kwatanta da 33.66% a Fabrairu 2024, an samu ragi wanda ya kai kaso 8.51%.
Idan aka duba daga wata zuwa wata, hauhawar farashin kayan abinci a birane ya sauka zuwa kashi 2.40% a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan
"An takura wa shugaban kasa" Seyi Tinubu ya kare mahaifinsa daga sukar 'yan adawa
Bugu da kari, alƙaluma sun nuna cewa matsakaicin hauhawar farashi na watanni 12 a birane ya kai 32.22% a Fabrairu 2025, wanda aka samu karin 4.28 fiye da na Fabrairu 2024 (27.93%).
Mutanen karkara sun samu sauƙi
A banagren karkara, farashin kayan abinci a Fabrairu 2025 ya sauka zuwa kashi 19.89%, wanda ke nufin an samu raguwar 10.09% daga 29.99% da aka samu a Fabrairu 2024.
A ƙididdigar wata wata kuma, hauhawar farashi kayan abinci a karkara ya dawo kashi 1.16% a watan Fabrairu 2025.

Asali: Getty Images
Matsakaicin hauhawar farashi kayan abinci cikin shekara guda ya ɗaga zuwa kaso 27.94%, wanda ya fi na watan Fabrairu 2024 (24.61%) da kaso 3.33%.
A 2024, Najeriya ta fuskanci hauhawar farashi mafi girma cikin shekaru 28, sakamakon tuge tallafin fetur da karya darajar Naira.
Farashin abinci ya karye da azumi
A wani rahoton, kun ji cewa farashin kayan abinci ya karye a kasuwannin Najeriya tun daga shigowar watan azumin Ramadan na shekarar 1446.
Wasu masana sun yi hasashen haka tun kwanaki da suka gabata da suke ganin hakan na da alaƙa da yawan kayan abinci da ake shigo da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng