Karfin Hali: 'Yan Bindiga Sun Sace Babban Jami'in Dan Sanda a Abuja

Karfin Hali: 'Yan Bindiga Sun Sace Babban Jami'in Dan Sanda a Abuja

  • Wani babban jami'in dan sandan kasar nan, CSP Modestus Ojiebe ya fada hannun ‘yan bindiga a Abuja yayin da motarsa ta lalace
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi wa CSP Ojiebe da matarsa fashi, daga bisani suka gano ashe jami'in dan sanda ne
  • Wannan ta sa suka tilasta masa shiga motarsu kirar Mercedes-Benz mai launin toka, sannan suka bar iyalinsa a kusa da bariki
  • Tuni rundunar 'yan sandan ta shirya domin tsaurara tsaro tare da zurfafa bincike don ceto jami'in nata da ya fada mawuyacin hali

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - 'Yan bindiga sun yi karfin halin sace wani jami’in dan sanda a babban birnin tarayya Abuja, ba tare da fuskantar cikas ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bayanin yadda bindigogi kusan 4,000 suka bace a karkashin kulawarta

Wani babban jami’in rundunar ‘yan sanda mai mukamin CSP, Modestus Ojiebe, wanda ke aiki a jihar Kwara, ya fada hannun ‘yan bindiga a kan babbar hanyar Kubwa da ke Abuja.

Police
Yan sanda sun sace jami'in dan sanda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

ZagazOlaMakama ya wallafa a shafinsa na X cewa wa lamarin ya faru ne da dare a ranar Lahadi, lokacin da motar Ojiebe, kirar Toyota Corolla, ta lalace kusa da barikin Dei-Dei.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace jami’in ‘yan sanda

Yayin da CSP Modestus Ojiebe ke kokarin gyara motarsa, sai wata mota Mercedes-Benz mai launin toka, dauke da mutum hudu masu makamai, ta tsaya a bayansa.

Majiyoyin sun bayyana cewa maharan sun bincika Ojiebe da matarsa, suka kwace wayoyinsu da katunan ATM.

Sai dai bayan da suka gano katin shaidarsa na dan sanda, nan take suka tilasta masa shiga motarsu, suka tafi da shi cikin gaggawa, suka kuma bar matarsa da motarsu a wurin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

'Yan sanda sun fara bincike kan sace jami’insu

Bayan faruwar lamarin, rundunar 'yan sandan da ke yankin Dawaki ta samu kiran gaggawa, nan take ta tura tawagar sintiri zuwa wurin da abin ya faru.

Yan sanda
Ana kokarin ceto dan sandan da 'yan bindiga suka sace Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A halin yanzu, ‘yan sanda sun kara tsaurara bincike tare da aiwatar da tsauraran bincike na duba ababen hawa da ke shigowa da fita daga Abuja don ceto jami’in da kuma kama masu laifin.

Zuwa yanzu, ba a samu labarin nasarar kama wanda ake zargi ba, ko kuma gano inda CSP Modestus Ojiebe yake ba.

Rundunar 'yan sanda ta dauki alhakin batan makamai

A baya, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta gargadi manyan jami'anta dake jihohin Najeriya a kan wasarere da makamai a hannun 'yan koyo domin gujewa batansu.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, a cikin sanarwar da ya aika zuwa wasu jihohin kasar nan, ya ce daga yanzu, za a rika daukar mataki a kan batan bindigu.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Gargadin ya biyo bayan bincikin kwamitin majalisa a kan batan makaman da suka kusa kai 4,000, wadanda rundunar ta ce wasu bata gari ne suka yi awon gaba da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.