Kama Daliban Jami’ar OAU: Zanga-Zanga Ta Barke a Ofishin EFCC

Kama Daliban Jami’ar OAU: Zanga-Zanga Ta Barke a Ofishin EFCC

  • Kungiyar daliban jami'ar Obafemi Awolowo ta gudanar da zanga-zanga a ofishin hukumar EFCC na shiyyar Ibadan
  • Akalla dalibai 70 ne jami'an hukumar EFCC suka cafke a Ile-Ife bisa zargin su da aikata laifukan damfara a intanet
  • Sai dai kungiyar dalibai (SUG) ta jami'ar ta yi wa ofishin EFCC tsinke tare da bukatar a sako daliban da aka kama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Osun - Daliban jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, a ranar Laraba, sun yi wa ofishin hukumar EFCC shiyyar Ibadan tsinke, inda suka fara zanga zangar nuna rashin jin dadin yadda jami'an hukumar suka yi awon gaba da 'yan uwansu dalibai.

Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, jihar Osun
Daliban jami'ar OAU sun yi zanga zanga a ofishin hukumar EFCC kan daliban da aka kama Hoto: Ibrahim Lawal
Asali: Depositphotos

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya tattara rahoton yadda daliban, wadanda suka isa ofishin hukumar a manyan motoci guda uku, da kuma bas bas guda uku, suka yi wa ofishin tsinke domin ganin an sako daliban da hukumar ta kama.

Kara karanta wannan

Daga karshe hukumar EFCC ta haramtawa jami'anta kai samame da daddare

Dalilin da yasa daliban OAU ke zanga-zanga a ofishin EFCC

NAN ya kuma ruwaito cewa shuwagabannin kungiyar daliban jami'ar ne suka jagoranci wannan zanga zangar, kamar yadda jaridar Punch ta tabbar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika shuwagabannin kungiyar daliban sun bayyana cewa babu wata tattaunawa tsakanin hukumar EFCC da Jami'ar OAU kan wannan zargi da hukumar ke yi wa daliban makarantar na cewar suna damfara a intanet.

Sumamen da EFCC takai Ile-Ife da adadin daliban da aka kama

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa akalla dalibai 70 ne jami'an EFCC suka yi awon gaba da su a wani sumame da suka kai gidajen kwanan dalibai da ke wajen makaranta, a daren ranar Laraba.

Majiyoyi daga Ile-Ife sun tabbatarwa NAN cewa jami'an EFCC sun kai sumame a dakunan kwanan dalibai na Fine Touch da Superb, da ke rukunin gidaje na Oduduwa, inda suka kama daliban.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kwashi shugaban NLC Ajaero zuwa asibiti, cikakken bayani

Shugaban kungiyar daliban jami'ar, Abass Ojo, ya ce kungiyar ta tattara sunayen dalibai 72 da hukumar EFCC ta kama tare da yin awon gaba da su, tare da motoci, wayoyi da kwamfutocin su.

Jerin Sunaye: EFCC Ta Kama Dalibai 69 Kan ‘Damfara Ta Intanet’ a Ile-Ife

Jami'an hukumar EFCC shiyyar Ibadan sun cafke dalibai sittin da tara, 69, da ake zargin su da aikata laifuka na damfara a yanar gizo, a cewar Legit Hausa.

An cafke su ne a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, 2023 a rukunin gidaje na Oduduwa da ke Ile-Ife, jihar Osun biya bayan sahihan bayanai da hukumar ta samu na ayyukan damfara da suke aikata wa a yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel