Abin Boye Ya Fito Fili: Sanata Ya Yi Fallasa kan Rigimar Akpabio da Natasha
- Bayanai na ta ƙara fitowa fili kan taƙaddamar shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- Sanata Peter Nwaebonyi ya yi zargin cewa Natasha ta yi barazanar kunyata Akpabio kafin ta fito ta zarge shi da neman cin zarafinta
- Peter Nwaebonyi ya bayyana cewa Natasha ta yi barazanar ne bayan an sauya ta daga muƙamin shugaba a wani kwamitin majalisar dattawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata Peter Nwaebonyi ya yi yi sabon zargi kan taƙaddamar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Godswill Akpabio.
Sanatan ya yi zargin cewa Natasha ta yi barazanar kunyata shugaban majalisar dattawa, kwana ɗaya kafin ta fito fili ta zarge shi da cin zarafinta ta hanyar lalata.

Asali: Facebook
Sanata Nwaebonyi ya jefi Natasha da zargi
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na Sunrise Daily.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Peter Nwaebonyi shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattawa kuma ɗan majalisa mai wakiltar Ebonyi ta Arewa.
A ranar 28 ga Fabrairu, Sanata NatashaɓAkpoti-Uduaghan ta zargi Akpabio da yunƙurin neman yin lalata da ita a ofishinsa da kuma gidansa da ke Akwa Ibom.
Meyasa Natasha ke jin haushin Akpabio?
Peter Nwaebonyi ya yi zargin cewa zargin da Sanata Natasha ta yi na cin zarafi, ya biyo bayan rasa kujerarta ta shugabar wani kwamiti a majalisar, bayan an yi garambawul kan shugabancin kwamitoci.
Mataimakin mai tsawatarwa ya ce Natasha ba ta ji dadin sauya ta daga shugabancin kwamitin majalisar dattawa kan 'Local Content' zuwa kwamitin harkokin ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ba.
“Sanata Natasha ita ce shugabar kwamitin majalisar dattawa kan 'Local Content', muƙamin da take jin daɗinsa."
"Sai dai, a majalisar dattawa, daga lokaci zuwa lokaci, ana canza shugabannin kwamitoci, ana yin sauyin shugabanci, kwamitinta ya shiga cikin wannan sauyi kamar yadda sauran shugabanni ma suka fuskanta."

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha ta fitar da saƙo mai zafi bayan dakatar da ita a Majalisa
- Sanata Peter Nwaebonyi
Sanata Natasha ta fifita buƙatunta
Nwaebonyi ya ce, maimakon ta maida hankali kan nauyin da ke kanta na wakiltar al’ummarta, Natasha ta fifita buƙatunta fiye da muradun mazaɓarta, wanda hakan ne ya kai ga zargin cin zarafin da ta yi.
“Bari na faɗa muku, kwana ɗaya kafin ta bayyana a tashar Arise tana wannan iƙirari na cin zarafi, ta kira wani sanata (Sanata Sani Musa na jihar Neja).
"Ta buƙaci ya faɗawa shugaban majalisar dattawa ya dawo da ita matsayin shugabar kwamitin 'Local Content'. Ta yi barazanar cewa idan ba a yi hakan ba, za ta kunyata shugaban majalisar Dattawa.”
"Ya kamata ƴan Najeriya su san wannan. Sanata Natasha na zargin cin zarafi ne saboda ta rasa shugabancin kwamitin 'Local Content', ba wai don Sanata Akpabio, ko wani sanata daban ya ci zarafinta ba."
- Peter Nwaebonyi
Akpabio ya fadi wani sirri kan auren Natasha
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya faɗi abin da ya faru da shi a ranar auren Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa a daren auren Natasha, ya kwana ne a masana'antar simintin Dangote saboda fitilun filin jirgin saman Kogi sun lalace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng