'Ku Bar Kashe Su': Matar Rikakken Ɗan Bindiga Ta Tura Sako ga Sojojin Najeriya

'Ku Bar Kashe Su': Matar Rikakken Ɗan Bindiga Ta Tura Sako ga Sojojin Najeriya

  • Wata matashiya da ake zargi matar ɗan ta’adda ce ta fitar da bidiyo tana roƙon sojoji ka da su kashe ‘yan bindiga da suka kama
  • A cewarta, sojoji suna aikata barna kamar yadda ‘yan bindiga ke yi, don haka bai dace a kashe su ba idan aka cafke su a cikin daji
  • Bidiyon da aka wallafa a dandalin X ya jawo cece-kuce, wasu ke suka, yayin da wasu ke ganin sojoji sun gaza game da lamarin tsaro
  • Wannan na zuwa ne yayin da sojoji ke ci gaba da matsa wa yan ta'adda musamman a Arewacin Najeriya domin kakkabe su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Nigeria - Wata da ake zargin watakila matar wani rikakken dan ta'adda ce ta fitar da faifan bidiyo da take shawartar sojojin Najeriya.

Wannan mata ta nuna damuwa kan yadda sojoji ke hallaka mazajensu (yan bindiga) a cikin daji musamman a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan

Matar ɗan bindiga ta roki sojoji alfarma
An gano wani bidiyon matar rikakken ɗan bindiga tana rokon sojoji kan kisan mazajensu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Matar ɗan bindiga ta roki sojojin Najeriya

Zagazola Makama ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa na X a daren jiya Litinin 3 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, matar ta roki sojojin Najeriya ka da su hallaka wadanda suka cafke tana nufin yan bindiga a daji.

A cewarta, ba ‘yan bindiga ba ne kaɗai ke aikata miyagun laifuffuka ba, sojoji ma suna da laifi idan suka kashe su.

A bidiyon mai tsawon dakika 15, matashiyar ta fara da kwada wata sallama:

"Assalamu alaikum, wabarka tuhu, sojoji idan kun samu mazajenmu a cikin fashi ko barna ka da ku kashe su.
"Kuma ku na barna tun da idan kun kama mutum kuna kashe su, ina fada muku ku daina."

Wannan bidiyo ta matar ya fitar ya jawo maganganu a kafofin sadarwa inda wasu ke ganin laifin sojoji da suka kyale ta'addanci.

Yadda matar dan ta'adda ta yi bidiyo ga sojojin Najeriya
Matar wani rikakken dan bindiga ta roki sojoji su bar kashe mazajensu. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Martanin wasu yan Najeriya kan bidiyon:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

Abdulrasheed:

"Ya kamata a bi diddigi domin cafke ta saboda ta fuskanci hukunci daidai da ita."

PAN-AFRICANIST:

"Abin da na gagara ganewa shi ne yadda mutanen nan ke rayuwa a daji amma sun fi sojoji da suka shafe lokaci suna samun horo a kasashen waje wayo."

condottiero:

"Saboda tsoron shan guba, ku kauracewa shan fura da nono a wuraren da yan bindiga suke da yawa."

ELOLO:

"Shegiya ko sallama ba ta iya ba, kazama kawai."

Sadiq, Ibrahim:

"Ban ga laifin ta ba ko kadan, tana rayuwa ne da kuma jin dadin abin da mijinta ke aikatawa."

Yadda 'yan ta'adda ke addabar jama'a

‘Yan bindiga sun addabi yankunan Arewacin Najeriya, inda suke kashe mutane ba tare da tausayi ba.

Wadannan ‘yan ta’adda suna kai hare-hare ga kauyuka, suna kona gidaje, kuma suna tilasta wa mutane barin muhallansu.

Akai-akai, sukan bude wuta kan matafiya a manyan hanyoyi, suna kashe wasu tare da yin garkuwa da wasu domin neman kudin fansa.

Kara karanta wannan

Ana neman Turji, wani ɗan bindiga da yaransa sun ba da mamaki, sun mika wuya

Wasu daga cikin munanan hare-haren da suka aikata sun hada da farmakin da suka kai gidajen mutane da daddare, inda suke kashe mazaje, suna yi wa mata fyade, sannan su sace yara da matasa domin su nemi kudin fansa.

A wasu lokuta, idan iyalai sun kasa biyan kudin fansa, sukan kashe wanda suka sace don nuna tsananinsu.

Ayyukan tsageru a makarantu

Makarantu da gidajen ibada ba su tsira ba. A lokuta da dama, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai masu tarin yawa, suna tilasta iyayensu ko hukumomi su biya makudan kudade.

Harin da suka kai a Zamfara, Katsina, da Kaduna sun yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba daruruwan iyalai da matsugunansu.

Kisan gilla da ‘yan bindiga ke yi ya jefa jama’a cikin tsoro da damuwa, inda mutane da dama suka daina yin tafiye-tafiye ko fita daga gidajensu da dare.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Wannan matsala na bukatar gaggawar daukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Dalibar jami'a ta mutu a hannun yan bindiga

A baya, kun ji cewa dalibar da yan bindiga suka sace watanni hudu baya ta riga mu gidan gaskiya duk da cika sharudan maharan da iyayenta suka yi.

Matashiyar mai suna Zarah Abubakar Shehu tana karatu a Jami’ar Tarayya Gusau, ta mutu bayan an biya kudin fansa na miliyoyi da kuma ba yan ta'addan babura.

An ce maharan sun fara neman ₦35m daga bisani suka amince da ₦10m, amma bayan an biya, sun ƙi sakin ta, suna neman ƙarin kayayyaki daga iyayenta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng