Aminu Ado Bayero Ya Ziyarci Basarake, Ya Magantu kan Jarabawar da Suka Shiga
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara jihar Bauchi domin halartar babban taro, tare da nuna godiya ga Sarkin da majalisarsa
- Aminu Ado ya jaddada cewa jarabawa daga Allah ne kuma ya yi kira ga mutane su ci gaba da addu'a don samun mafita mai alheri
- Basaraken ya yi addu'ar Allah ya kawar da duk wata matsala, ya kuma gode wa jama'a bisa addu'o'in su da goyon baya ga masarautar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Bauchi - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya kai ziyara jihar Bauchi domin halartar babban taro.
Aminu Ado ya kai ziyara fadar Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu inda ya yi masa godiya da sauran yan Majalisar masarautar.

Asali: Twitter
Aminu Ado ya ce suna cikin jarabawa
Basaraken ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a shafin X a yau Juma'a 24 ga watan Janairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, Aminu Ado ya jaddada cewa Allah na jarrabar bayinsa a duk lokacin da ya ga dama.
Basaraken ya ce yana da tabbacin Allah zai kawo karshen wannan jarabawa da suke ciki cikin kankanin lokaci.
Tabbacin da Aminu Ado ke da shi
"Za mu yi amfani da wannan dama, mu kara jawabi cewa duk abin da ya faru da kai Ubangiji ne ya ƙaddara.
"Kuma jarabawa ce da ke zuwa ga bayinsa duk inda ya ga dama, mun gode masa da wannan jarabawa da ake ciki.
"Muna da yakinin za mu ci wannan jarawaba, don haka mu ci gaba da addu'a Allah tabbatar da mafi alheri a rayuwa."
- Aminu Ado Bayero
Basaraken ya yi addu'ar Allah ya tabbatar da kawar duk wasu abubuwa marasa dadi a tare da su nan ba da jimawa ba.
Aminu Ado Bayero ya godewa Sarkin Bauchi da da sauran yan Majalisarsa da ma al'ummar kasa baki daya kan addu'o'i da goyon bayansu.
Aminu Ado ya godewa Sarkin Bauchi, masarautarsa
"Ina godewa Sarkin Bauchi, godiya ta ba za ta kare a gare shi ba, ina godewa dukkan yan Majalisar sarki da sauran al'ummar wannan kasa.
"Bayan gaisawa da dan uwanmu, muna yi masa fatan alheri kan taron da za a yi a wannan gari mai albarka.
"Muna addu'ar Allah ya sa a yi wannan taro lafiya ya kuma kamar da kowa da kowa gida lafiya."
- Cewar Aminu Ado Bayero
Daga bisani, Aminu Ado Bayero ya yi addu'ar Allah ya jikan shugabanni da malaman addini da iyaye da suka riga mu gidan gaskiya.
Aminu Ado ya yi ta'azziyar rasuwar matar sarki
Kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar ta’aziya ga Sarkin Keffi, Alh. Dr. Shehu Cindo Yamusa na Jihar Nassarawa.
Ziyarar ta’aziyar ta biyo bayan rasuwar matar Sarkin Keffi, wacce ta kasance ginshiki a masarautar Keffi da ke Nasarawa.
Asali: Legit.ng