Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Bi Sahun Abba, Ya Dauki Nauyin Dalibai 1100

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Bi Sahun Abba, Ya Dauki Nauyin Dalibai 1100

  • Shugaban karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano, Kwamared Abdullahi Ghali Basaf ya dauki nauyin dalibai 1,100 domin yin karatun NCE
  • A yayin da ciyamomin Kano 44 suka cika kwanaki 100 a kan mulki, Kwamared Abdullahi Basaf ya lissafa ayyukan da ya shimfida a Kumbotso
  • Wannan yunkurin na shugaban karamar hukumar na zuwa ne yayin da gwamnatin Abba Kabir ta sake tura 'ya'yan talakawa karatu waje

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Zababbun shugabannin kananan hukumomin Kano, sun shafe kwanaki 100 kenan a kan mulki, tun bayan rantsar da su a karshen Oktobar 2024.

A cikin ciyamomi 44 na Kano ne aka samu shugaban karamar hukumar Kumbotso, Kwamared Abdullahi Ghali Basaf da ya dauki nauyin karatun dalibai 1100.

Shugaban karamar hukumbotso ya magantu da ya dauki nauyin karatun dalibai 1100
Kano: Shugaban karamar hukumar Kumbotso ya dauki nauyin karatun 'ya'yan talakawa 1100. Hoto: Abdullahi Ghali Basaf
Asali: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, yayin bikin murnar cikarsa kwanaki 100 a kan mulki, Kwamared Basaf ya ce ya himmatu wajen inganta ilimi.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki matsaya kan buƙatun kirkiro sababbin jihohi 31 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ciyaman ya dauki nauyin karatun dalibai 1100

Bayan hawansa mulki, shugaban karamar hukumar ya ce ya kafa shirin ilimi na BASAF domin tallafawa al'ummar Kumbotso su samu ilimi cikin sauki.

A karkashin shirin ne, Kwamared Basaf ya ce:

"Mun yi nasarar nemawa dalibai 1100 gurbin karatu a kwalejin ilimi ta Sa'adu Zungur, tare da daukar nauyin karatun nasu, don basu damar samun kwalin NCE."

Shugaban karamar hukumar, ya yabawa hukumar gudanarwar kwalejin, karkashin Dakta Kabiru Gwarzo kan yadda suke kula da daliban da ya dauki nauyin karatunsu.

Dalilin daukar nauyin karatun daliban

A zantawarsa da Legit Hausa, Kwamared Abdullahi Ghali Basaf ya ce ta hanyar daukar nauyin karatun dalibai ne zai gina rayuwarsu.

"Sanin kowa ne cewa ilimi shi ne gishirin zaman duniya, don haka, ko a iya mutum 1,100 na tsaya, ina da tabbacin iliminsu zai amfani gaba daya karamar hukumar Kumbotso.
"Wannan somin tabi ne kawai, domin muna kokarin ganin cewa dubunnan matasa 'yan asalin Kumbotso sun samu ilimi kafin wa'adin mulkinmu ya kare."

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi? APC ta sanar da ficewa daga zaben ƙananan hukumomi, ta jero dalilai

Shugaban karamar hukumar, ya ce shirin ba da ilimi na BASAF na zakulo dalibai daga dukkanin gundumomin Kumbotso ba tare da nuna wariya ba.

Shugaban karamar hukuma ya yi magana da ya dauki nauyin karatun dalibai 1100 a Kano
Shugaban karamar hukumar Kumbotso, tare da gwamnan Kano, Abba Yusuf. Hoto: Abdullahi Ghali Basaf
Asali: Facebook

Baya ga daukar nauyin karatun daliban, Kwamared Basaf ya kuma kaddamar da ayyukan gyaran makarantu, rabon kayan karatu da sauran shirye-shiryen ilimi.

Wasu ayyukan shugaban karamar hukumar

A bangaren kiwon lafiya, rahoto ya nuna cewa Kwamared Abdullahi Basaf, ya dauki nauyin dalibai domin karantar ilimin jinya, da kuma raba magunguna a mazabu 11.

Hakazalika, shugaban karamar ya tausayawa 'yan Kumbotso ta hanyar shirin ba da katin ganin likita kyauta, da sanya fitila mai amfani da hasken rana a asibitin Panshekara.

An ce shugaban karamar hukumar, ya ba matasan da suka je horon aikin dan sanda kyautar N1.2m domin karfafa masu gwiwa, da kuma gyaran motocin 'yan sintiri na Kumbotso.

Kwamared Abdullahi Basaf, ya kuma ba makarantun Islamiya 15 tallafin N2m, tare da gyaran masallatai da makarantun islamiya a wasu sassan Kumbotso.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kaddamar da kwamishinonin haraji guda 50

A bangaren gina matasa kuwa, an ce shugaban karamar hukumar, ya nemawa matasa da dama aiki a kamfanonin masu zaman kansu, da tura su karatun koyon sana'o'i.

Duba sanarwar a nan kasa:

Abba ya tura 'ya'yan talakawa 1001 karatu kasar waje

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin dalibai 1001 zuwa kasashen Indiya da Uganda don karo karatu.

Gwamna Abba Kabir ne ya kaddamar da wannan shiri wanda tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kirkiro, da nufin inganta ilimin 'ya'yan talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.