Kano: Dan Majalisar NNPP Ya Ba Dalibai 512 a Mazabarsa Kyautar Miliyoyin Naira, Ya Gigita Jama’a

Kano: Dan Majalisar NNPP Ya Ba Dalibai 512 a Mazabarsa Kyautar Miliyoyin Naira, Ya Gigita Jama’a

  • Dan majalisar tarayya da ke wakiltar mazabar Fagge, ya ba dalibai 512 daga makarantun jami'a da na sakandire tallafin miliyoyin naira
  • Mohammed Bello Shehu ya ce ya ba daliban wannan tallafi don su biya kudin makarantar su, la'akari da tsadar rayuwar da ake ciki a kasar
  • Haka zalika, Shehu ya ware naira miliyan 50 don gina makarantar firamare a yankin Rijiyar Lemo, inda ya ce babu ko daya a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Fagge a jihar Kano, Mohammed Bello Shehu ya biya wa dalibai 512 kudin makaranta da ya kai naira miliyan 38.

Daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin akwai daliban jami'ar ABU Zariya, UDU Sokoto, FUD Jigawa, SH, Kano, da sauran makarantu a fadin kasar.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama fasto da wasu mutane biyu kan damfara a Kogi

Dan majalisar Fagge, Mohammed Bello Shehu
Dan majalisar Fagge a jihar Kano ya rabawa dalibai 512 miliyoyin naira kuma zai gina firamare. Hoto: muhammad.b.shehu
Asali: Facebook

Shirin Mohammed Shehu ga daliban mazabarsa

Dan majalisar ya bayyana hakan a ranar Alhamis a zantawarsa da manema labarai a Kano, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Mohammed Shehu, zai ci gaba da kyautatawa al'ummar mazabarsa ma damar yana a zauren Majalisar tarayyar, musamman a fannin ilimi.

Jaridar ta ruwaito cewa dan majalisar ya kashe naira miliyan 22 don biyan kudin jarrabawar NECO ga daliban makarantu sakandire na mazabar.

Dan majalisar zai gina makarantar firamare a Rijiyar Lemo

Ya kuma ce tuni ya kammala shiri na gina makarantar firamare a Rijiyar Lemo da ke cikin mazabarsa, a jihar, rahoton jaridar Blueprint.

Aikin gina makarantar zai lakume naira miliyan 50, kuma tuni dan majalisar ya ware kudin, a cewar rahoton jaridar.

Ya ce:

"Babu makarantar firamare ko daya a Rijiyar Lemo, mun kuma dukufa kan hakan. Mun samar da filin yin ginin, kuma za mu yi ginin makarantar irin na zamani."

Kara karanta wannan

Na kusa da gwamnan PDP ya ɗauki matakin karshe kan ƴan majalisa 25 da suka koma APC

NSCDC ta kama fasto da wasu mutum biyu kan damfara a Kogi

A wani labarin, hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta kama wani Fasto Chimezie bisa laifin damfarar wani mutum naira miliyan daya.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta kuma kama Faruk Abdullahi da Attahiru Abu bisa laifin damfarar abokan kasuwancin su a jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel