'Can Ta Matse Musu': Ribadu Ya Fusata da Aka Wulakanta Hafsan Tsaron Najeriya a Ketare
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya soki gwamnatin Canada dakile hafsan tsaro, Christopher Musa shiga kasar
- An gayyaci Janar Musa da tawagarsa zuwa taron girmamawa ga tsofaffin sojoji a Canada, amma wasu ba su samu damar shiga ba
- Ribadu ya kira matakin da rashin girmamawa, yayin da hafsun ya yi kira ga Najeriya ta tsaya da kafafunta a fagen siyasa na duniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya soki gwamnatin Canada saboda hana 'visa' ga Hafsan Tsaron Najeriya, Christopher Musa.
Nuhu Ribadu ya nuna bacin ransa kan matakin gwamnatin kasar inda suka hana Janar Musa da wasu manyan jami’an soja shiga cikinta.

Asali: Facebook
Yadda Canada ta wulakanta hafsan tsaron Najeriya
Jami’an sun shirya halartar wani taro a Kanada na girmama tsofaffin sojoji, amma ba duka suka samu bisa ba, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya haifar da martani mai zafi daga hukumomin Najeriya inda suke ganin hakan rashin girmama wa ne.
Nuhu Ribadu da Musa sun yi jawabi ne a wani taro na farko na shekara-shekara na kungiyar daliban tsofaffin makarantar tsaro ta kasa (AANISS) a Abuja.
Ribadu ya fusata da matakin gwamnatin Canada
Ribadu ya sake jaddada muhimmancin yin kokarin bunkasa Najeriya, yana mai cewa wannan al’amari ya kara masa kwarin gwiwa wajen kawo cigaba.
Har ila yau, Ribadu yaba wa Musa kan jagorancin da yake bayarwa wajen yaki da matsalar tsaro, tare da kira ga hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
"Na yaba da yadda ka fito fili ka fadi cewa Canada ta hana ka bisa, can ta matse musu, koda yake abin yana da zafi kuma rashin girmamawa ne, mu mutane masu zaman lafiya ne kuma masu karfi, ya kamata mu gyara kasarmu."
- Nuhu Ribadu
Janar Musa ya fadi yadda lamarin ya afku
A bangarensa, Janar Musa ya jaddada bukatar Najeriya ta tsaya da kafafunta a duniya.
Janar Musa ya ce an gayyace shi da tawagarsa zuwa taron girmamawa amma aka hana wasu shiga, yana mai cewa lamarin abin takaici ne, cewar TheCable.
“An gayyace mu tare da tawagarmu, rabinmu sun je, amma an hana rabin shiga wanda hakan abin takaici ne.
“Wannan darasi ne ga Najeriya ta tsaya da kafafunta, ta tsaya da karfi a matsayin kasa, kuma kada a sake raina ta.”
- Janar Christopher Musa
Ribadu ya gargadi Naja'atu kan bidiyon TikTok
Mun ba ku labarin cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya gargadi Naja’atu Muhammad ta janye kalamanta game da zarginsa a bidiyon TikTok.
Naja’atu ta zargi Ribadu da goyon bayan Bola Tinubu, wanda a baya ya soka a lokacin da yake shugaban EFCC da cewa yana dagacikin mafi rashin gaskiya a 'yan siyasa.

Kara karanta wannan
"An ba Tinubu gurguwar shawara," Ɗan Majalisa ya tona kura kuran da aka gano a ƙudirin haraji
Daga bisani, Naja'atu ta yi martani inda ya ce ba za ta janye kalamanta ba kuma a shirye take ta kare kanta saboda tana da hujjoji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng