Sauƙi Ya Ƙara Bayyana da Musulmi Suka Fara Shirye Shiryen Azumin Watan Ramadan

Sauƙi Ya Ƙara Bayyana da Musulmi Suka Fara Shirye Shiryen Azumin Watan Ramadan

  • Farashin kayayyakin amfanin yau da kullum ya fara araha a kasuwanncin Maiduguri yayin da azumin Ramadana ke gabatowa
  • Rahoto ya nuna farashin abinci kamar shinkafa, wake, masara da sauransu ya karye a kasuwannin jihar Borno da aka yi girbi
  • Wasu dai na ganin za a iya ƙara samun sauƙi nan gaba, wasu kuma sun nuna farin cikinsu da rahusar da aka samu dab da azumi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Maiduguri - Kasa da kwanaki 20 gabanin watan Ramadan, shagunan sayayya da kasuwanni sun fara cika a Maiduguri, babban burnin jihar Borno.

Musulmai na azumi daga fitowar rana har zuwa faduwarta a cikin Ramadan, wata mafi daraja a kalandar Musulunci.

Kayan abinci.
Farashin kayan abinci ya ƙara karyewa a kasuwannin Maiduguri yayin da aka fara shirin azumin Ramadan Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sai dai, sabanin shekarun baya da farashin kayayyaki ke tashi sosai kafin Ramadan, a bana kuwa sauka suke yi, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

An bindige limamin da ke ba yan luwadi mafaka da daurin gindi a masallaci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ramadan: Farashin abinci ya sauka a bana

A wani bincike da aka gudanar ranar Lahadi a kasuwannin Litini na Gamboru/Custom, da kasuwar titin Baga, an gano yadda abubuwa ke ƙara araha.

Binciken ya nuna cewa farashin kayan abinci kamar shinkafa, masara, wake, sukari, da gyada sun ragu da kashi 5 zuwa 6 cikin 100 a cikin watanni biyu da suka gabata.

A baya, buhun shinkafa ƴar gida mai nauyin kilo 50, ana sayar da shi tsakanin N90,000 da N95,000, amma yanzu ya ragu zuwa N84,000–N85,000.

Buhun sukari kilo 50 ya sauka daga N81,500 zuwa N80,500. Farashin buhun wake mai nauyin kilo 100 kuma ya ragu daga N140,000 zuwa N90,000.

Har ila yau, wasu kayan lambu masu saurin lalacewa sun karye, kwandon tumatir da ake sayarwa akan N25,000 a baya, yanzu yana tsakanin N7,500 da N12,000.

Barkono (kilo 100) ya sauka daga N90,000 zuwa N60,000, yayin da buhun albasa mai nauyin kilo 100 ya dawo N50,000.

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

Mutane na fatan ƙara samun saukin abinci

Yayin da wasu ke amfani da wannan dama don siyan kayan bukata kafin farashin ya tashi, wasu kuma na siyan kaɗan, suna fatan cewa farashin zai ci gaba da raguwa.

Wani ɗan kasuwa a kasuwar Custom, Goni Modu ya ce:

"Alhamdulillah, muna ƙara gode wa Allah, farashi yana sauka a hankali. Tiyar shinkafa ta ragu da kusan N200. Haka wake ma ya ragu, amma farashin sukari har yanzu yana da tsada.
Muna fatan farashin zai ci gaba da sauka saboda har yanzu yana da tsada idan aka kwatanta da ƙarfin kasarmu."

Sai dai, wasu sun ce sun je kasuwa ne kawai domin duba farashin, suna fatan sauƙi zai kara samuwa nan gaba kaɗan.

Yadda musulmi suka fara sayayya

Umar Mohammed ya ce ya sayi kaɗan yayin da yake jiran ganin ko farashi zai ƙara raguwa nan gaba.

“Babu wani abu da za a yi murna da shi, musamman idan muka duba yadda farashin ke tashi tun shekaru biyu da suka gabata. A baya muna sayen waɗannan kayayyakin da ragin kusan kashi 50 cikin 100 ko sama da haka.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

"Ba a samu wani canji mai yawa a albashinmu ba. Kamar yadda kake gani, na sayi kaɗan ne, ba na son yin gaggawa. Ina fata farashin zai ci gaba da raguwa kafin Ramadan,” in ji shi.

Wani magidanci, Hudu Lawal ya tabbatarwa Legit Hausa cewa kaya sun fara sauka a kasuwa amma har yanzu dai mutane na fama da matsin rayuwa.

Mutumin ya ce:

"Kayan abinci sun yi sauƙi kwanan nan amma idan aka kwatanta da farashin kafin zuwan wannan gwamnatin, babu wani sauƙi. Mu fa abin da muke so a soke waɗannan tsare-tsaren.
"Yanzu ko da kayan nan sun yi araha, nan gaba za a ƙara haraji, me kuke tunanin zai faru? Ga kuɗin kira an ƙara, komai kan talaka yake karewa, Allah dai ya kawo mana sauƙi."

Farashin hatsi ya karye a Ɗandume

A wani labarin, kun ji cewa farashin hatsi ya faɗi warwas a wani rahoto da aka samu daga kasuwar Ɗandume da ke jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Shaidar APC ya ba jam'iyya kunya a kotu, ya ce an yi magudi a zaben Gwamna

An ruwaito cewa farashin masara, dawa, gero, waken suya da sauran makamantansu sun sauka idan aka kwatanta da baya a kasuwar Ɗandume.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262