An Bindige Limamin da Ke ba Yan Luwadi Mafaka da Daurin Gindi a Masallaci

An Bindige Limamin da Ke ba Yan Luwadi Mafaka da Daurin Gindi a Masallaci

  • An harbe Imam Muhsin Hendricks, wanda ake ganin shi ne liman na farko mai bayyana kansa a matsayin dan luwadi, kusa da Gqeberha a Afirka ta Kudu
  • 'Yan sanda sun ce mutane biyu masu rufe fuska sun harbe shi tare da guduwa, kuma ana ci gaba da binciken dalilin kisan
  • Wata Kungiya ta yi Allah wadai da kisan, tana kira ga hukumomi su bincika ko an kashe shi ne saboda kiyayya ga auren jinsi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gqeberha, Afirka ta Kudu - Rahotanni sun ce an harbe Muhsin Hendricks, wanda ake ganin shi ne limami na farko mai bayyana kansa a matsayin dan luwadi.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 15 ga watan Janairun 2025 a kusa da birnin Gqeberha a Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

An harbe limamin da ke ba yan luwadi mafaka
Yan sanda sun fara bincike kan kisan limami da ke goyon bayan yan luwadi. Hoto: ILGA World.
Asali: Facebook

An bindige wani limami kan alaka da yan luwadi

The Guardian ta ce limamin yana cikin mota tare da wani mutum lokacin da wata mota ta tare su, sannan wasu mutane biyu fuska a rufe suka bude musu wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan harbin, wadanda suka kai harin sun tsere, kuma aka gano cewa an kashe Hendricks wanda yake zaune a bayan motar.

Jami’ar ‘yan sanda ta tabbatar da gaskiyar wani bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna harin da aka kai masa a Bethelsdorp.

“Babu wanda ya san dalilin kisan, kuma bincike yana gudana, muna rokon masu bayanai su taimaka."

- Cewar ‘yan sanda

Wata kungiya ta roki hukumomi kan lamarin

Wata Kungiya mai suna ILGA ta yi Allah wadai da kisan, tana kira ga hukumomi su gudanar da cikakken bincike kan abinda suka kira laifin kiyayya.

Hendricks ya fito fili a matsayin mai goyon bayan auren jinsi tun 1996, kuma yana jagorantar masallacin Al-Ghurbaah a Wynberg kusa da Cape Town.

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

Masallacin na bayar da damar ibada ga Musulmai masu goyon bayan auren jinsi da mata masu fama da wariya, kamar yadda shafinsa na yanar gizo ya bayyana.

Afirka ta Kudu na da kaso mai yawa na kisan kai, inda aka yi kisan mutane 28,000 a cikin shekara guda zuwa watan Fabrairun 2024, cewar The Indian Express.

An hallaka baturen da ya kona Alkur'ani

Kun ji cewa wasu rahotanni sun nuna cewa an harbe Salwan Momika a Sweden, mutumin da ya haddasa tarzoma bayan ya ƙona Alƙur'ani a shekarar 2023.

Firaministan Sweden ya ce akwai yiwuwar kisan na da alaƙa da wasu ƙasashen waje, kuma ana binciken lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.