Yayin da aka Aika Farfesa Usman Kurkuku, Kotu Ta Wanke Femi Fani Kayode
- Kotu da ke Ikeja, Legas, ta wanke tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, daga zargin da hukumar EFCC ke yi masa
- Mai shari’a Olubunmi Abike-Fadipe ta ce EFCC ta kasa tabbatar da laifin Fani-Kayode, wanda ya sa kotu ta amince da bukatar lauyansa
- Bayan hukuncin, Fani-Kayode ya bayyana farin cikinsa da godiya, yana mai cewa ya shafe shekaru ana fama da shari'ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kotu ta musamman da ke sauraron manyan laifuka a Ikeja, Legas, ta wanke tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, daga zargin da ake masa.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Fani-Kayode bisa zargin ya gabatar wa kotu takardar rashin lafiya ta jabu.

Asali: Facebook
Channels Television ta ruwaito, Mai shari’a Olubunmi Abike-Fadipe ce ta yanke hukunci inda ta wanke Fani-Kayode bayan ta amince da bukatar lauyansa na cewa ba shi da laifi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari’ar ta bayyana cewa EFCC ta gaza gabatar da hujjojin da za su tabbatar da cewa Fani-Kayode ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.
Kotu ta amsa bukatar Fani-Kayode
Punch News ta wallafa cewa kotu ta amince da bukatar lauya Mista Kayode, Norrison Quakers (SAN), na cewa wanda ya ke kare wa bai aikata laifin komai ba.
A cikin hukuncinta, Mai shari’a Abike-Fadipe ta ce masu gabatar da kara sun kasa kawo wasu mutane da suka karbi kudade daga hannun wanda ake tuhuma.
Haka kuma EFCC ta ko lauyan da ya ce Fani-Kayode ne ya umarce shi da ya kai takardun lafiyan zuwa Babban Kotun Tarayya.
Ta ce:
"Na yi nazari sosai kan shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar, kuma ban ga inda aka nuna cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin da ake zarginsa da shi ba."
Fani-Kayode ya ji dadin hukuncin kotu
Da yake magana da manema labarai bayan hukuncin, Fani-Kayode ya bayyana godiya da farin cikinsa kan yadda kotu ta wanke shi.
Ya ce ya sha fama da shari'ar da aka shafe shekaru 18 ana yinsa, kuma yanzu ya ji dadin yadda aka tabbatar da gaskiyarsa.
Zargin da EFCC ke yi wa Kayode
Kafin wannan hukunci, EFCC ta gurfanar da Fani-Kayode kan tuhumar laifuka 12 da suka shafi amfani da jabun takardun lafiya.
An yi zargin cewa ya mika takardar ga Mai shari’a Daniel Osiagor na Babban Kotun Tarayya da ke Ikoyi, Legas, inda ake tuhumarsa da zamba da ya shafi Naira biliyan 4.9.
EFCC ta maka Fani-Kayode a gaban kotu
A baya, mun ruwaito hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta sanar da shirin sake gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, a gaban kotu.
Hukumar yaki da rashawar na zargin Fani-Kayode da barnatar da kuɗaɗen gwamnati har Naira biliyan 4.6. Lauyan hukumar, Rotimi Oyedepo (SAN), ya shaidawa alkali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng