Fani-Kayode Ya Caccaki Dino Melaye Kan Kayen da Ya Sha a Zaben Kogi: “Allah Sarki Dino, Ya Zo Na 3”
- Jama'a na ci gaba da cece-kuce kan kayen da Dino Melaye ya sha a zaben gwamnan Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba
- Da yake magana kan ci gaban, Fani-Kayode ya caccaki Melaye kan zuwa na uku da ya yi a zaben
- Ya bukaci jigon na PDP da ya yi ritaya gaba daya daga siyasa yayin da ya bayyana cewa kayen da ya sha ya nuna "ta kare masa a siyasa"
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigon jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya yi wa Dino Melaye ba'a a kan kayen da ya sha a zaben jihar Kogi da aka kammala.
![Fani Kayode ya caccaki Dino kan faduwa a zaben Kogi Fani Kayode ya caccaki Dino kan faduwa a zaben Kogi](https://cdn.legit.ng/images/1120/84425e8e277b2cc1.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
FFK ya ce Dino bai da tasiri a siyasa
A cikin wasu jerin wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, FKK ya bayyana kayen da Dino ya sha a zaben gwamnan na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, a matsayin gagarumin koma baya a harkar siyasarsa.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/c66a1bb1f324e8ac.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Reno Omokri ya fallasa gaskiyar dalilin da yasa NLC ta shiga yajin aikin gama gari
Fani-Kayode ya bayyana cewa duk da cika bakin Dino, ya dandana kudarsa a zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon na APC ya tuna yadda dan takarar na PDP ya caccaki Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mutanensa a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 har ma ya yi barazanar keta mutuncin uwargidan shugaban kasa amma duk da haka ya kasa samun kuri’u masu ma’ana a zaben.
Sai dai kuma, ya bukaci tsohon sanatan da ya yi ritaya gaba daya daga siyasa.
FKK ya ce:
"Allah sarki Dino. Cikin kuri'u 751,000 da aka bai iya samun kuri’u 47,000 ba. Wato kusan kashi 5 cikin 100. Abun da ya fi muni shine ya zo na uku a tseren kuma ma wasu sun ce na hudu! Abun tausayi!
"Wannan shine mutum da aka taba zaba a matsayin dan majalisar wakilai kuma sanata! Toh a yau yana inda yake kuma ta kare masa a siyasa. Ta yaya manya suka fadi! Da alamu farin zakin Kogi ya cika alkawarinsa kuma ya yi masa ritaya daga siyasa gaba daya.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/a97795ae9dad67e3.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
"Ko na yi zabe ko ban yi ba bai da amfani": Dino Melaye ya magantu kan yadda APC ta murde zaben Kogi
"Zuciya ta na tare da shi."
Dino ya magantu kan zaben Kogi
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa dan takarar PDP, Sanata Dino Melaye ya magantu game da kuri'arsa a aben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Tsohon sanatan na Kogi ya amsa wata gayyatar hira da Channels TV a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, yana mai cewa kada kuri'arsa ko akasin haka a zaben da aka kammala bai da amfani.
Asali: Legit.ng