Hantar Tinubu Ta Kada, Ya Roki Kotu kan Bukatar Tsige Shi a Majalisa, Ya Jero Dalilai

Hantar Tinubu Ta Kada, Ya Roki Kotu kan Bukatar Tsige Shi a Majalisa, Ya Jero Dalilai

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kotun tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da karar da ke neman majalisar dokoki ta fara shirin tsige shi daga mulki
  • Lauyan da ya shigar da karar ya zargi Tinubu da danniya, yana mai cewa tilasta hana zanga-zanga ta lumana, babban dalili ne na tsige shugaban kasa
  • Tinubu da Ministan Shari’a sun bukaci kotu ta kori karar, suna masu cewa mai karar bai da hurumin shigar da ita saboda bai nuna hakkin da aka take masa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mayar da martani kan korafin da aka shigar da neman a tsige shi.

Tinubu ya bukaci Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da wata kara da ke neman tilasta wa majalisar dokoki fara shirin tsige shi daga mukaminsa bisa zargin take hakkin dan Adam.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sabuwar jami'ar fasaha a Najeriya

Tinubu ya mayar da martani kan korafi da aka yi domin tsige shi a majalisa
Bola Tinubu ya bukaci kotu ta yi wata da korafi da ke gabanta kan neman tsige shi a majalisa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Lauya ya bukaci majalisa ta tsige Bola Tinubu

Wani lauya mai suna Olukoya Ogungbejeshi ya shigar da korafin yana mai zargin gwamnatin Tinubu da take hakkin dan Adam, cewar Vanguard.

Ogungbeje, ya bukaci kotu ta ayyana cewa hana zanga-zanga ta lumana da gwamnatin Tinubu ta yi tsakanin Agusta 1 zuwa 10, 2024, babban laifi ne da ke sa a iya tsige shugaban kasa.

Amma a cikin takardar kin amincewa da karar da Tinubu da Ministan Shari’a suka gabatar, sun ce wanda ya shigar da karar bai da hurumin yin hakan, saboda bai bayyana wani hakki nasa da aka take ba.

Sun kuma ce doka ta tanadi cewa mutum ne kawai da aka take hakkinsa ke da damar shigar da kara a kotu, ba wakilcin wasu ba.

Gwamnatin Tinubu musanta take hakkin dan Adam

A gefe guda, wani jami’in ma’aikatar shari’a, Gbemga Oladimeji, ya bayyana a kotu cewa gwamnatin Tinubu ba ta tauye hakkin kowa ba, domin ana ba da damar yin zanga-zanga cikin lumana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta sauya magana, ta ce babu batun karin kudin wutar lantarki

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a James Omotosho, ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Maris, 2025.

Alkalin ya yi haka ne don bai wa lauya mai kara damar mayar da martani kan kin amincewar da gwamnati ta yi, Punch ta ruwaito.

Gwamantin Tinubu ta musanta shirin kara kudin wuta

Kun ji cewa Fadar Shugaban Kasa ta musanta rahotannin da ke cewa akwai shirin karin kudin wutar lantarki da 65% a kwanan nan .

Olu Arowolo Verheijen, mai ba shugaba Bola Tinubu shawara kan makamashi, ta bayyana cewa an fahimci kalamanta ba daidai ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.