"Ko Ya Musulunta ne?": Sanata Ya Ba Mutane Mamaki, Ya Yi Sallah Tare da Musulmi
- Mutane sun yi mamakin yadda Sanata Otunba Gbenga Daniel ya shiga cikin musulmi aka yi sallar jana'iza da shi a jihar Ogun
- Sanata Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun ya halarci jana'izar marigayiya ƴar majalisar tarayya, Adewumi Onanuga da ta rasu a watan Janairu
- Sai dai sama da makonni biyu bayan lamarin, wata majiya ta ce sanatan wanda ke bin addinin kirista, ya yi sallar ne saboda kusancinsa da marigayiyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma sanata mai ci, Otunba Gbenga Daniel, ya ba mutane da dama mamaki yayin da ya halarci ibada ta Musulunci.
Sanata Daniel, wanda aka sani da bin addinin Kiristanci da kuma shiga harkokin coci, ya ba jama’a mamaki da aka ga ya halarci jana'iza tare da Musulmai.

Asali: Facebook
Jaridar Tribune Nigeria ta rahoto cewa sanatan ya samu halartar jana'izar ƴar majalisar tarayya, Hon Adewumi Onanuga, wadda Allah ya yi wa rasuwa kwanan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Daniel ya shiga an yi sallah da shi
Ƴar majalisar mai wakiltar mazaɓar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa daga jihar Ogun, wacce aka fi sani da Ijayi ta rasu ne ranar Laraba, 15 ga watan Janairu, 2025.
Taron jana’izar marigayiyar ya samu halartar manyan mutane, ƴan siyasa da malaman addinin Musulunci.
Sai dai an fara ce-ce-ku-ce bayan ganin tsohon gwamna, Sanata Daniel, wanda kirista ne ya halarcu jana'izaɗ musamman yadda ya shiga aka mata sallah da shi.
Sanatan, tare da wasu fitattun mutane da suka halarci jana’izar, sun yi Sallar Janaza, watau addu’ar neman gafara da rahama ga mamaci a addinin Musulunci.
Makusancin sanatan ya faɗi dalilin faruwar lamarin
Wata majiya kusa da sanatan ta bayyana cewa matakin da ya dauka ba sabon abu ba ne, domin ana ganinsa a matsayin mutum mai yawan hakuri da juriya a harkar addini.
Ya kuma bayyana cewa yana da manyan mukaman addinin Musulunci, wanda suka haɗa da Aare Musulumi na Ipokia da kuma Amuludun Adeen na Ikija.
Har ila yau ya ce Sanata Daniel ya shiga an yi sallar Jana'iza da shi ne saboda yadda rasuwar ta taɓa shi da kuma kusancinsa da marigayiyar.
Tsohon ɗan Majalisa ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan Majalisar Wakilan tarayya daga jihar Oyo, Hon. Temilola Segun Adibi ya riga mu gidan gaskiya.
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana rasuwar Segun Adibi, babban jigo a jam’iyyar PDP a matsayin babbar rashi ga jihar Oyo baki ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng