Mataimakin Shugaban Malaman Kungiyar Izala Ya Rasu a Filato
- Allah ya yi wa Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Plateau, Malam Ibrahim Umar, rasuwa a garin Jos bayan rashin lafiya
- An bayyana cewa za a gudanar da jana'izarsa da misalin karfe 9:00 na safiyar nan a Masallacin Mai Allo, reshen Nasarawa a Jos ta Arewa
- Al'umma da dama sun nuna alhinin rasuwar tare da tura sakon ta'aziyya ga iyalansa da al'ummar Musulmi har ma da kungiyar Izala
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - An sanar da rasuwar Mataimakin Shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izala na biyu a Jihar Plateau.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Malam Ibrahim Umar ya rasu ne cikin dare a garin Jos bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Asali: Facebook
Babban dan agajin Izala, Hamza Muhammad Sani ne ya sanar da rasuwar a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana ta da cewa babban rashi ne ga al'ummar musulmi baki daya.

Kara karanta wannan
Bayan shafe tsawon lokaci a kan sarauta, kotu ta tsige mai martaba sarki a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin ya rasu ne a babban asibitin koyarwa na Jos, inda ya yi jinya kafin Allah ya karbi rayuwarsa.
Rashin ya girgiza al'umma da dama musamman mabiya Izala da wadanda suka amfana da iliminsa.
Za a yi jana'izarsa a jihar Filato
Za a gudanar da jana'izar marigayin Malam Ibrahim Umar da misalin karfe 9:00 na safiyar nan a Masallacin Mai Allo da ke reshen Nasarawa a Jos ta Arewa.
An tabbatar da cewa an dauko gawarsa daga babban asibitin koyarwa na Jos domin shiryawa jana'izar wadda ake sa ran dimbin mutane za su halarta.
Abokan aiki da dalibai sun nuna alhini
Al'umma da dama sun tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da kuma kungiyar Izala. Sun bayyana kaduwar su tare da addu'ar Allah ya gafarta masa ya sanya shi a Aljannar Firdausi.
Haka zalika, abokan aikinsa da daliban da suka amfana da iliminsa sun bayyana cewa Malam Ibrahim Umar ya kasance mutum mai ilimi, dattaku, da kyawawan halaye.
Rayuwa da ayyukan marigayin
Malam Ibrahim Umar ya shahara da wa'azi da karantarwa a fadin jihar Plateau da ma Najeriya baki daya. Ya kasance fitaccen malami wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi.
Baya ga wa'azi da karantarwa, ya kasance cikin masu rubuce-rubuce a shafin Facebook domin fadakar da al'umma kan al'amuran addini da rayuwa ta gari.
Addu'ar gafara ga marigayin
Daga karshe, al'ummar musulmi suna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa Malam Ibrahim Umar, ya sanya kabarinsa ya kasance wuri mai haske.
Ana rokon Allah ya ba wa iyalansa da kungiyar Izala da Sheikh Sani Yahaya Jingir ke jagoranta hakurin jure babban rashin, ya kuma sanya Aljannar Firdausi ta kasance makomarsa.
Izala ta shirya taron kasa a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala ta shirya wani taro na musamman da ta saba yi duk shekara a birnin tarayya Abuja.
A yayin taron, kungiyar za ta nemi tallafin kudi da ya kai Naira biliyan 1.5 domin bunkasa harkokin ilimi kuma an gayyaci manyan kasa ciki har da Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng