An Kama 'Yan Bindigar da Suka ba Basarake Kudi domin Kafa Sansanin Ta'addanci

An Kama 'Yan Bindigar da Suka ba Basarake Kudi domin Kafa Sansanin Ta'addanci

  • Dakarun rundunar soja ta 6 karkashin Operation Whirl Stroke sun kashe ɗan ta’adda tare da ƙwato tarin makamai a Jihar Taraba
  • Sojojin sun cafke mutane 23, ciki har da maza 19 da mata 4, bayan fafatawa da ‘yan ta’addan da suka buɗe musu wuta yayin samamen
  • Bincike ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun biya ₦1.5m ga wani basarake a ƙauyen Amar domin su kafa sansaninsu a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a kokarinta na yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, bayan da ta kashe wani babban ɗan ta’adda.

Bayan kashe babban dan ta'addan, an kama wasu da dama a karamar hukumar Karim Lamido na jihar Taraba.

Taraba
An kama tarin 'yan ta'adda a Taraba. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an kama wasu da dama cikin 'yan ta'addar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samamen ya gudana ne bisa bayanan sirri da suka nuna motsin wasu ‘yan ta’adda da ke boye a Angwan Bala da ke yankin Kambari, inda suka yi arangama mai zafi da sojoji.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ya fitar, an bayyana cewa sojojin sun yi nasarar ƙwato tarin makamai da babura daga hannun ‘yan ta’addan.

Dalilin samamen da nasar da aka samu

Dakarun runduna ta 6 tare da haɗin guiwar dakarun Operation Whirl Stroke sun kai samame maboyar ‘yan ta’adda da ke Angwan Bala a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2025.

An gudanar da aikin ne bisa sahihin bayanan sirri kan motsin wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne, inda dakarun suka ci karo da su a maboyarsu.

Da isar sojojin sansanin, ‘yan ta’addan sun buɗe musu wuta, amma dakarun sun mayar da martani mai ƙarfi wanda ya haifar da kisan ɗaya daga cikinsu.

An ruwaito cewa bayan sojoji sun saki wuta kan 'yan ta'addar, guda 23 sun mika wuya, ciki har da maza 19 da mata hudu.

Makaman da sojoji suka kwato a Taraba

Bayan samun nasarar cafke ‘yan ta’addan, dakarun sojin sun gudanar da bincike a sansanin inda suka gano tarin makamai masu haɗari.

An ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda huɗu, harsasai, an samu bindiga kirar Pistol, bindigogi biyu na gida, adduna guda 28, wukake da gatari 48, da kuma babura guda 16.

'Yan ta'adda sun biya basarake kudi

Binciken farko ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Filato zuwa Taraba domin cigaba da ta'addanci.

Haka zalika an ruwaito cewa sun biya wani basarake a ƙauyen Amar Naira miliyan 1.5 domin samun damar kafa sansani a yankin, wanda ya zama cibiyar shirya hare-harensu.

An yabi sojoji bayan kashe 'yan ta'adda

Kwamandan rundunar, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yabawa dakarun da suka gudanar da aikin, yana mai cewa nasarar ta nuna jajircewar rundunar wajen tabbatar da tsaro.

"Samamen da muka kai yana nuna cewa ba za mu lamunci kasancewar masu aikata laifuffuka a cikin Taraba ba.
"Muna da niyyar kawar da duk wani abu da zai hana zaman lafiya,"

- Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa

Ya kara da cewa rundunar na da cikakken shiri na ci gaba da kai irin wadannan hare-hare domin kakkabe duk wata barazana ga zaman lafiyar al’umma a yankin.

An yanka mata da miji a jihar Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun shiga wani kauye cikin dare sun kashe mutane da dama.

'Yan sandan jihar Filato sun tabbatar da cewa 'yan ta'addar sun kashe mutanen kauyen ciki har da mata da miji da aka yi wa yankan rago.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng