Rufe iyakoki: Garuruwan da ke kusa da iyakokin kasar sun fara fuskantar matsalar man fetur

Rufe iyakoki: Garuruwan da ke kusa da iyakokin kasar sun fara fuskantar matsalar man fetur

- Kwanaki biyar kacal bayan bayar da umarnin hana kai man fetur garuruwan da ke da kusanci da iyakokin kasar nan, 'yan Najeriya sun fara kokawa

- Mazauna jihohin Ogun, Legas, Adamawa, Katsina da Sokoto sun bayyana yadda farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a yankunan

- Idan ba zamu manta ba, har kungiyar 'yan kasuwar man fetur na kasar sun yi kirafi a kan lamarin

Kwanaki biyar bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bada na hana kai man fetur garuruwa masu kilomita 20 kusa da iyakokin kasar nan, mazauna garuruwan kusa da iyakokin kasar nan irinsu jihohin Ogun, Legas, Adamawa, Katsina da Sokoto sun fara kukan illar da wannan umarnin ya aka bada.

Jaridu da dama sun ruwaito yadda hukumar kwastam ta kasa ta bada sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta haramta kai man fetur duk gidajen mai da ke da nisan kilomita 20 zuwa iyakokin kasar nan.

DUBA WANNAN: Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

Kamar yadda rahoto ya nuna, jihohin Ogun, Legas, Adamawa, Katsina da Sokoto sun fara fadawa mummunar matsalar rashin man fetur tare da tashin gwauron zabi da yayi a yankunan.

Umarnin ya kawo rashin man fetur a Ihhnbo, Ilase, Ajegunle, Idiroko da Agosasa na karamar hukumar Ipokia ta jihar Ogun, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito.

A bayan mun kawo muku cewa Dan majalisar jihar Legas, Victor Akande ya ce nan gaba 'yan Najeriya za su yabawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan rufe iyakokin kasar na kasa da ta yi.

Mista Akande mai wakiltan mazabar Ojo I a majalisar Legas ya yi wannan furucin ne a hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Talata a Legas.

Dan majalisar, wanda shine shugaban kwamitin shari'a, kare hakin 'dan adam da sauraron korafin Jama'a ya ce rufe iyakokin kasar zai amfani Najeriya a bangarorin tsaro da tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel