Gwamna Abba Ya Fadi Rashin Adalcin da Ake Yi Wa Fulani, Ya ba Su Mafita

Gwamna Abba Ya Fadi Rashin Adalcin da Ake Yi Wa Fulani, Ya ba Su Mafita

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna cewa babu dacewa kan yadda ake ɓata sunan al'ummar Fulani a ƙasar nan
  • Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa al'ummar Fulani sun ba da gudunmawa mai tarin yawa wajen ci gaban Najeriya
  • Gwamnan ya buƙaci al'ummar Fulani da su haɗa kansu waje ɗaya, su kare haƙƙinsu da kuma ƴancin da suke da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan ɓata sunan Fulani da ake yi a ƙasar nan.

Gwamna Abba ya bayyana cewa ko kaɗan bai dace ba yadda ake yi wa Fulani baƙin fenti a ƙasar nan.

Gwamna Abba ya koka kan bata sunan Fulani
Gwamna Abba ya ce bai dace ba yadda ake bata sunan Fulani Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga ƙungiyar Tabital Fulaku International, reshen jihar Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya koka kan ɓata sunan Fulani

Gwamna Abba wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya tabbatar da ƙudirin gwamnatin jihar na marawa ƙungiyar baya a ƙoƙarinta na haɗa kan Fulani a ƙasar nan.

Ya kuma yi kira ga shugabannin Fulani da su kasance masu jajircewa wajen ɗora matasa a kan hanya, inda ya jaddada muhimmancin hakan wajen ci gaban al'umma.

Mataimakin gwamnan ya bayyana damuwa kan yadda ake ɓata sunan Fulani a wasu kafafen yaɗa labarai, duk da irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban Najeriya.

"Al’ummar Fulani sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya, inda suka samar da manyan jagorori a fagen siyasa, ilimi, fasaha, shari’a, da tsaro."
"A yanzu haka, Bafulatani ne ke riƙe da muƙamin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro."

- Aminu Abdulsalam Gwarzo

Ya kuma shawarci shugabannin kungiyar da su nemi goyon baya daga jami’an gwamnati waɗanda asalinsu Fulani ne.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi ɓaram ɓarama a siyasar APC, ya saki layi a gaban Ganduje

Ya kuma caccaki yadda ake ɓata sunan Fulani a ƙasar nan.

"Abin takaici ne yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke ɓata sunan Fulani. Fulani suna bayar da gudunmawa mai yawa a ɓangaren noma da sauran fannonin tattalin arziƙi."
"Makiyaya ne ke tallafawa tattalin arziƙinmu. Wannan ɓata sunan da ake yi musu bai dace ba."

- Aminu Abdulsalam Gwarzo

An ba gwamnatin tarayya shawara

Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi kira ga gwamnatin tarayya, musamman hukumomin tsaro, da su ɗauki matakan magance yadda ake ɓata tarihin Fulani da gudunmawar da suke bayarwa.

Ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin Fulani a Najeriya da su haɗa kai, su manta da bambance-bambancensu, su yi aiki tare domin kare haƙƙin al’ummar Fulani da ci gabansu.

NLC ta karrama Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Kano, ta karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hanyar ba shi lambar yabo.

Ƙungiyar NLC ta ba Gwamna Abba lambar yabo 'gwamnan da ya fi nuna kishin ma'aikata' kan yadda yake kula da ma'aikatan gwamnati a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng