“Ya Yi Ta’aziyya”: Bashir Ahmad Ya Fadi Dalilin Rashin Zuwan Buhari Jana’izar Dada

“Ya Yi Ta’aziyya”: Bashir Ahmad Ya Fadi Dalilin Rashin Zuwan Buhari Jana’izar Dada

  • Wasu mutane sun yi ta ce-ce-ku-ce a kafofin sadarwa kan rashin halartar tsohon shugaba Muhammadu Buhari jana'izar Dada
  • Sai dai tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad ya bayyana musababbin rashin halartar mai gidan nasa jana'izar da aka yi a Katsina
  • Wannan na zuwa ne bayan rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa Yar'Adua a asibitin jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi magana kan rashin zuwan zuwansa jana'izar Hajiya Dada.

Ana yadawa a kafofin sadarwa cewa Buhari yana Daura amma bai halarci jana'izar mahaifiyar marigayi Umaru Musa Yar'Adua ba.

Bashir Ahmad ya kare Buhari kan rashin zuwa jana'izar Hajiya Dada
Bashir Ahmad Ya Fadi Dalilin Rashin Zuwan Buhari Jana’izar Hajiya Dada a jihar Katsina. Hoto: @BashirAhmaad.
Asali: Twitter

Jana'izar Dada: Bashir Ahmad ya kare Buhari

Kara karanta wannan

"A yi amfani da tsarin IBB": Janar Akilu ya ba Tinubu shawarar magance rashin tsaro

Bashir Ahmad ya fadi dalilin hakan a shafinsa na X a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024 domin cirewa mutane kokwanto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon APC ya ce ya gani ana ta cece-kuce kan rashin zuwan Buhari jana'izar a Katsina inda ya ce akwai dalili.

Ya ce tsohon shugaban bai Najeriya shi ne dalilin rashin samun damar halartar jana'izar da aka yi.

Musabbabin rashin zuwan Buhari jana'izar Dada

"Na gani ana ta yada cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yana Daura amma bai halarci jana'izar Hajiya Dada ba, mahaifyar babban abonkinsa, marigayi Janar Shehu Yar'Adua da tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'Adua a Katsina."
"Tsohon shugaban kasa yanzu haka ba ya Najeriya wannan shi ne dalilin rashin halartar jana'izar, sannan ya tura sakon ta'aziyya ga iyalansu."

- Bashir Ahmad

Bashir Ahmad ya fadi illolin TikTok

Kara karanta wannan

"Uwa ce ga kowa," Dan majalisa ya yi jimamin rasuwar mahaifiyar shugaba 'Yar'adua

Kun ji cewa Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana takaicin yadda 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a shafin Tiktok.

Wannan na zuwa ne bayan bullar jerin bidiyon wasu 'yan ta'adda su na nuna kudin fansar da su ka karba a hannun jama'a da dama a Najeriya.

Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X cewa lamarin yadda miyagu ke baje hajarsu a shafin tiktok na nuni da cewa akwai matsala babba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.