Wata Naira Biliyan 9 da Aka Ware a Kasafin Kudin 2025 Ta Jafe Ministoci 2 a Matsala
- Majalisar tarayya ta sake gayyatar ministoci biyu da Darakta Janar na ofishin kasafin kudi domin su bayyana gabanta gobe Talata
- Ƴan Majalisa sun gayyaci ƙusoshin gwamnatin tatayya ne domin su mata bayani kan rashin warewa ma'aikatar ma'adanai isassun kuɗaɗe a kasafin 2025
- Da farko majalisa ta gayyaci ministan kasafi da tsare-tsare Atiku Bagudu amma ya ki amsa wannan gayyata a zaman ranar Litinin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar tarayya ta sake gayyatar Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun da ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu.
Majalisar ta gayyaci ministocin biyu su bayyana gabanta tare da Darakta-Janar na ofishin kasafin kudi, Tanimu Yakubu kan kuɗin da aka warewa ma'aikatar ma'adanai.

Asali: Twitter
Dalilin da Majalisa ta gayyato ministoci 2
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Majalisar ta kira ministocin ne domin su mata bayanin dalilin ware N9bn kacal ga ma'aikatar ma'adanai a kasafin 2025.

Kara karanta wannan
"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan majalisar sun cimma matsayar sake kiran ministocin a zaman kwamitin haɗin guiwa mai kula da ma'aikatar ma'adanai ƙarƙashin Sanata Sampson Ekong (PDP, Akwa Ibom ta Kudu).
Hakan dai na zuwa ne bayan Bugudu ya shure gayyatar da Majalisar ta masa tun farko kan wannan batu ƙarancin kudin da aka warewa fannin ma'adanai a 2025.
Ministan kasafi ya shure gayyatar Majalisa
A makon da ya gabata, kwamitin ya bukaci Atiku Bagudu ya bayyana gabansa a ranar Litinin don ya yi bayanin dalilin da yasa aka ware kuɗaɗen da suka yi wa ma'aikatar kaɗan.
Sai dai ministan bai halarci zaman ba yau Litinin, 20 ga watan Janairu, 2025, wanda ya sa ƴan Majalisar suka tura masa sakon gayyata karo na biyu.
Tun farko dai ministan ma'adanan ƙasa, Dele Alake ya ce Naira biliyan 9 da aka warewa ma'sikatarsa a kasafin kudin 2025 ba za su isa ba.
Ministan Tinubu koka kan ware N9bn
Ya bayyana hakan ne makon da ya gabata yayin kare kasafin ma'aikatar a gaban kwamitin haɗin guwa na Majalisa.
Kwamitin ya kuma ce wannan adadi na N9bn ba zai iya gudanar da ayyukan ma'aikatar ma'adanai tsawon shekara guda ba.
Shugaban kwamitin haɗin gwiwa ya ce,
“Mai girma minista, muna godiya da ƙoƙarin da ka ke yi wajen neman karin kuɗaɗe ga ma’aikatar a kasafin 2025, amma muna jin takaici cewa duk da waɗannan ƙoƙarin, ba a ƙara komai ba kan Naira biliyan 9 da aka tsara.”
Bisa haka kwamitin ya buƙaci dukkan waɗanda aka gayyata su tabbata sun halarci zaman gobe Talata.
An yi hatsaniya a Majalisar Tarayya
A wani labarin, kun ji cewa hayaniya ta barke a Majalisar Tarayya yayin zaman kare kasafin kuɗin ma'aikatar albarkatun man fetur na 2025.
Ƴan majalisar sun nuna ɓacin ransu ne bisa rashin zuwa da takardin kasafin kudin ma'aikatar man fetur a zaman kare kasafin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng