Sojoji Sun Samu Nasara a Kaduna, Tantiran Masu Safarar Makamai Sun Shiga Hannu
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin masu safarar makamai ne a jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin na rundunar Operation Safe Haven sun cafke mutanen ne guda biyu a ƙauyen Fadiya da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna
- Bayan cafke mutanen da ake zargin, dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai masu yawa da suka haɗa da bindigogi da alburusai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Dakarun sojojin sashe na bakwai na rundunar Operation Safe Haven sun kama wani shahararren mai safarar makamai tare da abokin aikinsa, a jihar Kaduna.
Dakarun sojojin sun ƙwace tarin makamai da alburusai yayin samamen wanda suka gudanar a jihar Kaduna.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Gabas da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka cafke masu safarar makamai
Dakarun sojojin sun gudanar da samamen ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Janairu, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu laifin.
Wata majiya ta bayyana cewa an cafke waɗanda ake zargin ne a ƙauyen Fadiya da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf.
Majiyar ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin a matsayin Timothy Yusuf mai shekaru 62 da ɗansa Timothy Obadiah.
A cewar majiyar, waɗanda ake zargin sun dade suna gudanar da ayyukan safarar makamai a yankin, lamarin da ya zama barazana ga tsaro
Sojoji sun ƙwato mugayen makamai
A lokacin samamen, sojojin sun ƙwace bindigogi 11, jigida ta bindigar AK-47 guda biyu da kuma harsasan NATO guda 60 masu kaurin 7.62mm.
“Masu laifin da makaman da aka ƙwace suna tsare don gudanar da bincike, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran mambobin ƙungiyar masu safarar makaman."
- Wata majiya
Wannan nasarar dai, na daga cikin ƙoƙarin gwamnati da jami'an tsaro wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a yankin.
Jami'an tsaro a Najeriya na ci gaba da ƙara zage damtse wajen kawo ƙarshen miyagu waɗanda ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar nan.
Karanta wasu labaran kan dakarun sojoji
- Sababbin bayanai sun fito kan ta'asar 'yan Boko Haram a sansanin sojoji da ke Borno
- Bello Turji ya shirya fito na fito da sojoji, ya kafa sabon sansani a jihar Zamfara
- "An shigo da ƴan ta'adda daga waje," Sojoji sun gano masu hannu a sababbin hare hare
- Sojoji sun yi bajinta, sun kawo karshen 'yan ta'adda masu yawa a Kebbi da Sokoto
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun yi dirar mikiya kan sansanonin ƴan bindiga a jihohin Keebi da Sokoto.
Sojojin waɗanda suka gudanar da samamen a wasu ƙananan hukumomin jihohin biyu, sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga masu yawa tare da lalata sansanoninsu.
Farmakin da gwarazan dakarun sojojin suka kai kan ƴan bindigan ya tilastawa da yawa daga cikinsu tserewa daga maɓoyarsu domin tsira da rayukansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng