Yan Bindiga Akalla 20 Sun Sheka Barzahu bayan Sojoji Sun Share Maboyarsu a Jihohi 2
- Sojoji sun samu nasarar kashe fiye da ‘yan ta’adda 20 tare da rusa sansanoninsu a jihohin Sokoto da Kebbi a kokarin kakkabe 'yan bindiga
- Ana tsaka da aikin ne, sai dakarun su ka yi kicibis da sabon sansanin 'yan ta'adda, inda su ka kame makamai da sauran kayan aikinsu
- Bayan tsawon shekaru hudu da aka bar garin Manja saboda ta’addanci, sojojin Najeriya sun kwato garin kuma jama'a sun fara komawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Sojojin Najeriya karkashin atisayen Operation Fansan Yanma sun yi wa ‘yan ta’adda da ke aiki a jihohin Sokoto da Kebbi ruwan wuta a sansanoninsu.
Sojojin sun yi gagarumin aikin a kananan hukumomi kamar su Illela, Tangaza, Gudu, Binji, da Silami a jihar Sokoto, sai kuma Augie, Arewa, Argungu, da Dandi a jihar Kebbi.

Asali: Facebook
AIT ta ruwaito cewa sojojin sun kashe fiye da ‘yan ta’adda 20 tare da rusa sansanoninsu, wanda hakan ya sa suka tsere daga maboyarsu domin tsira da rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji na kokarin dawo da zaman lafiya
Zagazola Makama ya wallafa cewa sojojin sun yi aiki tukuru a yankunan da suka hada da dazukan Tsauna, Bauni, da Sarma, tare da kakkabe maboyar ‘yan ta’adda.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin sun kora ‘yan bindigar da ke samun mafaka a kauyukan, wanda ya sa su ka tsere daga maboyarsu, kuma su ka ba makamansu.
A Sarma Ruga, an samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda fiye da 20 a wani zazzafan artabu da gungun ‘yan bindiga da su ka fuskanci fushin zaratan sojojin Najeriya.
An gano sabon sansanin ‘yan ta’adda
Bayanai sun nuna cewa sojoji sun gano wani sabon sansanin ‘yan ta’adda a kusa da Dutsen Mai Hills, kuma an yi nasarar kwace kayan masarufi da sauran kayayyakin da suka bari.
Sojojin sun ci gaba da gudanar da atisaye har zuwa Jaima, wani gari da ke kan iyakar kasar nan da sojojin kasar Nijar suna gudanar da sintiri a yankin.
Ta’addanci: Jama’a sun fara komawa gida
A wata sanarwa da rundunar sojoji ta fitar, ta ce sun yi nasarar kakkabe Manja, wani gari da aka kwashe shekaru hudu ana fama da ta’addanci da fashi a ciki.
Wannan nasara ta sa mutanen gari sun fara dawowa gida, suna nuna farin ciki da godiya ga sojojin Najeriya domin ba su damar ci gaba da rayuwarsu a gida.
Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda kofar rago
A wani labarin, kun ji cewa zaratan sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar wasu gungun ‘yan bindiga a wani atisaye na musamman da suka gudanar a jihohin Zamfara da Katsina.
Wannan aiki na ya zo ne a wani bangare na kokarin gwamnati na kawo karshen rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa maso Yamma, inda 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan
Bayan kisan masu kamun kifi 20, yan ta'adda sun hallaka kwamandan sojoji da wasu jami'ai
Atisayen ya shafi kauyuka kamar Dajin Gidan Goga a Zamfara da Dajin Jibia a Katsina, aka samu nasarori bayan an yi wa 'yan ta'addan kofar rago tare da zuba masu albusurai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng