Manufar Tinubu kan Kudirin Haraji Ta Kara Fitowa Fili, Doka Za Ta Fara Aiki a 2025

Manufar Tinubu kan Kudirin Haraji Ta Kara Fitowa Fili, Doka Za Ta Fara Aiki a 2025

  • Mai girma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shirya fara aiwatar da sababbin dokokin haraji a farkon watan Yulin 2025
  • Shugaban kwamitin gyaran haraji, Taiwo Oyedele ne ya bayyana hakan, ya ce ana sa ran Majalisa za ta amince da kidirin a zangon farko
  • Oyedele ya ce kafin cire tallafin fetur, akwai rufa-rufa a harkokin mai a Najeriya wanda ba zai yi wa goben tattalin arziki kyau ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Duk da ce-ce-ku-ce da sukar da ƴan Najeriya ke ci gaba da yi, kudirin harajin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai zama doka a rubu'in farko na 2025.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin haraji da tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa Majalisa na daf da aminta da kudirin gyaran haraji.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Taiwo Oyedele.
Hadimin Shugaba Tinubu ya ce za a fara aiki da sabuwar dokar haraji a farkon watan Yulin 2025 Hoto: Taiwo Oyedele
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 13 ga Oktoba, 2024, shugaba Tinubu ya nemi Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta duba tare da amincewa da dokoki huɗu na gyaran haraji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗannan kudirori sun jawo suka mai tsanani, musamman daga waɗanda suka kira kudirorin da babbar illa ga Arewacin Najeriya.

Kudirin harajin Tinubu zai zama doka

Ana sa ran Majalisar za ta dawo da tattaunawa kan waɗannan dokoki da zaran da dawo daga hutun da ta tafi tun bara watau 2024.

Sai dai kudirori sun samu goyon bayan ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), amma dai ta nuna shakku kan tsarin rabon harajin kaya na VAT.

A wani zama da suka yi a Abuja, gwamnonin sun gabatar da tsarin da ya kamata a yi amfani da shi wajen rabon VAT wanda suke ganin shi ne adalci.

Shugaba Tinubu ya kafe kan dokar haraji

Da yake jawabi a ƙarshen mako a taron The Platform, wanda Cibiyar Covenant Nation ta shirya, Oyedele ya ce za a fara aiwatar da dokokin gyaran harajin a watan Yuli.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

“Akwai bukatar na taɓo batun gyaran haraji. Muna sa ran za a amince da sake fasalin da muke son yi musamman dokokin gyaran haraji, a shekarar 2025.
“Muna sa ran za a amince da su kafin ƙarshen zangon farko na shekara. Don haka, muna sanar da masu biyan haraji su shirya tare da ƙarfafa kansu kafin dokar ta fara aiki daga ranar 1 ga Yuli,” in ji shi.

Gwamnatin baya ta yi rufa-rufa a tallafin mai

Dangane da batun tallafin mai, Oyedele ya ce kafin cire tallafin man fetur, ana tafiyar da harkokin mai ne a duƙunƙune, rahoton Channels tv.

Ya ce duk da cewa tallafin ya sa man fetur, wuta, da sauran abubuwa sun kasance masu rahusa amma akwai abin da aka ɓoye game da tattalin arziki wanda ba zai ɗore ba.

“Cire tallafin shi ne mafi kyawun shawara da muka yanke a matsayin ƙasa kuma yanzu za mu iya cewa tallafin ya tafi har abada," in ji Oyedele.

Kara karanta wannan

"A bar mu da talaucinmu": Shettima ya fadi matsayarsa kan dogara da tallafin turawa

Ƴan Majalisar Arewa sun shirya turjiya

A wani rahoton, kun ji cewa ƴan Majalisar tarayya na Arewacin ƙasar nan na shirin juyawa kudirin gyaran haraji baya idan suka koma hutu.

Rahotanni sun nuna cewa Majalisa za ta maiɗa hankali kan dokar kasafin kudin 2025 da kudirin gyaran haraji idan ta koma aiki a 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262