Yan Arewa Sun Dira kan Sanusi II bayan Sukar Tinubu, Sun Fadi Illarsa ga Najeriya
- Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya sha suka mai zafi kan kalaman sa game da manufofin tattalin arzikin Bola Ahmed Tinubu
- Kungiyar NPCD ta bayyana cewa kalaman Sarkin sun yi nuni da son zuciya da rashin sanin abin da ya dace game da tattalin arzikin kasa
- Shugaban kungiyar, Mohammed Yahaya ya ce Sarkin ya rasa hurumin yin tsokaci, inda ya ce tsohon gwamnan CBN ne ya kara jefa kasa cikin matsaloli
- Wannan na zuwa ne bayan basaraken ya ce ba zai taimaka wa gwamnatin ba musamman kan abubuwan da suka shafi tattalin arziki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya sha suka mai tsanani saboda kalamansa kan manufofin tattalin arziki na Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar Northern Patriotic Coalition for Democracy (NPCD) ta caccaki Sarkin ne bayan sukar yadda Tinubu ke mulkin Najeriya.

Asali: UGC
"Ba zan taimaki Tinubu ba" - Sanusi II
Shugaban kungiyar, Mohammed Yahaya ya fadi haka a ranar Juma’a, 17 ga Janairun 2025 a Abuja a cikin wata sanarwa da The Nation ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta ruwaito cewa Sarki Sanusi II ya ce yana da shawarwari da hanyoyin warware matsalolin tattalin arziki a karkashin gwamnatin Tinubu amma ba zai bayar ba.
Hakan ya jawo wa basaraken suka daga bangarorin kasar duba da yadda al'umma ke cikin wani hali na matsain tattalin arziki.
Kungiya ta zargi Sanusi II da ruguza Najeriya
Kungiyar NPCD ta ce kalaman Sarkin Sanusi sun yi kama da kokarin biyan bukatun kansa da kuma tsoma siyasa, The Sun ta tattaro.
Mohammed Yahaya ya ce Sarkin bai da hurumin bayar da shawara kan gwamnati duba da rawar da ya taka wajen kara tabarbarewar tattalin arzikin kasa.
Ya ce Sarkin ya ba da gudunmawa wurin ruguza tattalin arzikin kasar lokacin da yake shugabancin Babban Bankin Najeriya (CBN).
"Madadin yaba wa tsare-tsaren ko bayar da shawara domin inganta kasa, amma Sanusi II ya biye wa son ransa kawai."
"Yana magana kan matsaloli ba tare da kawo mafita ba, wannan ba halin wanda yake ikirarin yana kishin kasa ba ne, shin Sanusi II yana da matsala ne da tsare-tsaren ko dai wata manufa ce?"
- Cewar sanarwar
Kungiya ta yaba wa gwamnatin Bola Tinubu
Yahaya ya kara da cewa Sarkin ya nuna rashin fahimtar matsalolin tattalin arziki da kuma gazawar bayar da mafita.
Kungiyar NPCD ta yabawa Shugaba Tinubu kan gyaran tattalin arziki, musamman cire tallafin mai da sauran tsare-tsare inda ta ce masana tattalin arziki na duniya sun yaba da manufofin nasa.
Abba Hikima ya magantu kan kalaman Sanusi II
Kun ji cewa lauya a Kano, Barista Abba Hikima ya yi mamakin dalilin Sarkin Kano na kin taimakawa gwamnatin Bola Tinubu.
A makon jiya ne, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce ya na da hanyar warware matsalolin tattalin arzikin Najeriya.
Amma Sarki ya ce ba zai taimaka da komai ba saboda zargin da ya yi na cewa abokansa da ke gwamnatin ba shi dauke shi aboki ba.
Asali: Legit.ng