Abubuwa Sun Kwaɓe, Matatar Ɗangote Ta Ƙara Farashin Man Fetur a Najeriya

Abubuwa Sun Kwaɓe, Matatar Ɗangote Ta Ƙara Farashin Man Fetur a Najeriya

  • Matatar Ɗangote ta ƙara farashin litar man fetur daga N899 zuwa akalla N950 ga masu saye da yawa, ta ce ƙarin zai fara aiki yau Juma'a
  • Karin ya biyo bayan hauhawar farashin danyen mai a ƙasuwar duniya, musamman man Brent wanda kowace ganga ta kai $81.84
  • Sababbin farashin za su fara aiki daga ƙarfe 5:30 na yammacin ranar 17 ga Janairu, 2025, kuma za su shafi duk wani mai da ba a ɗauka ba kafin lokacin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Matatar Ɗangote ta sanar da ƙarin farashin litar man fetur daga N899 zuwa N955 a Najeriya.

Matatar attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, "sanarwar sauya farashin man fetur," yau Juma'a.

Dangote.
Farashin.man fetur ya tashi a matatar Ɗangote Hoto: Dangote Group
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sanarwar wadda ta fito ranar Juma'a, ta nuna cewa matatar Ɗangote ta faɗi sabon tsarin farashin wanda ta kasa zuwa gida biyu.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Ɗangote ta kara farashin fetur

Matatar ta bayyana cewa farashin sayen mai da yawa da ya kama daga lita miliyan 2 zuwa lita miliyan 4.99 ya koma N955 a kowace lita.

Masu siyan lita miliyan 5 ko fiye da hakan, matatar Ɗangote ta ce a yanzu za a rika sayar masu da kowace lita N950, kamar yadda sanarwar ta nuna.

Wannan sabon farashi ya nuna an samu ƙarin kashi 6.17%, ko N55.5 a kan kowace lita, idan aka kwatanta da farashin da aka yi rangwame N899.50 a watan Disamba na 2024.

Sabon tsarin farashin zai fara aiki yau

Sanarwar ta ƙara da cewa sababbin farashin za su fara aiki daga ƙarfe 5:30 na yammacin yau (Juma’a), kuma za su shafi duk wani man da ba a sayar da shi ba da kuma odar da ba a ɗauka ba.

Matatar Dangote ta bayyana cewa ta ɗauki matakin yin wannan karin ne sakamakon hauhawar farashin danyen mai a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

“Muna sanar da ku cewa daga karfe 5:30 na yammacin yau za mu fara amfani da sabon tsarin farashin man fetur a matatarmu."
“Ku sani cewa duk wani mai da ba a ɗauka ba har zuwa wannan lokacin za a sake ƙididdige farashinsa bisa sababbin farashin da aka sanar.
“Nan ba da jimawa ba za mu sanar da sauran abokan cinikayyarmu farashin kowane adadin mai bisa ƙarin da aka yi," in ji sanarwar.

Menene ya kawo ƙarin farashin fetur?

An ruwaito cewa wannan karin ya biyo bayan ci gaba da hauhawar farashin danyen mai na Brent, wanda shi ne ma’aunin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Farashin danyen mai na Brent a kan kowace ganga ya haura zuwa $81.84, mafi tsadar farashin tun da aka shigo shekarar 2025.

Wani mai sana'ar sayar da fetur a bakin titi a Katsina, Kabiru Dogo ya shaida wa Legit Hausa cewa bai yi tsammanin ƙarin kudin mai ba a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Ya ce tun bayan tsire tallafi ciniki ya ragu saboda mutane sun fara neman wata mafitar ko kuma rage amfani da fetur sai abin da ya zama dole.

Kabiru ya ce:

"Ragin da aka yi kwanakin baya ya yi wa mutane da yawa daɗi, an yi tsammnin zai ci gaba da yin ƙasa ne amma kwatsam muka ji an ƙara farashi, duk da akwai dalili amma ba mu yi zaton haka ba.
"Kuma ya kamata a sa ido kan ƴan kasuwa, lokacin da aka yi ragi a watan Disamba, an ce za a sayar da kowace lita N935 a gidajen mai, ni dai har yau ban ga inda mai ya dawo ƙasa da N1,000 ba a yankinmu."

Gwamnati na da hannu a karin farashi?

A wani labarin, kun ji cewa ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa a yanzu gwamnatin tarayya ba ta da hannu a ƙayyade farashin fetur.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun sanar da saukar farashin fetur bayan karyewar abinci

Ministan ya ce yanke farashin kowace litar da za a sayar fetur ya dogara ne ga yanayin yadda kasuwar mai ke tafiya a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262