Jerin Kabilun Najeriya da Suka Fi Yawan Yara da ba Su Zuwa Makarantar Boko

Jerin Kabilun Najeriya da Suka Fi Yawan Yara da ba Su Zuwa Makarantar Boko

  • Hukumar kula da ƙananan yara ta UNICEF ta gano Kanuri, Fulani, da Hausa sun fi fama da yaran da ba sa zuwa makarantar boko a Najeriya a bara
  • Rahoton ya nuna Arewa maso Yamma na da yara 8,044,800 da ba su zuwa makaranta, Arewa maso Gabas 5,064,400, Arewa ta Tsakiya kuma 2,115,800
  • Kabilar Kanuri na da yara 982,200 da ba su zuwa makaranta wanda ya kai kaso 24.6 sai Fulani 3,305,500 da 13.2% Hausa 8,110,400 da 11.72%

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Hukumar kula da da ƙananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana Kanuri, Fulani, da Hausa a matsayin kabilu mafi yawan yaran da ba su zuwa makarantar boko a 2024.

Rahoton hukumar UNICEF ya nuna cewa Arewa maso Yamma na da yara miliyan 8.04 da ba sa makaranta, Arewa maso Gabas miliyan 5.06, da Arewa ta Tsakiya miliyan 2.11.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun tarfa ƴan bindiga, sun hallaka sama da 100

Kabilun da suka fi yawan wadanda ba su zuwa makaranta
Hausa da Fulani sun fi kowa yawan yara da ba su zuwa makaranta. Hoto: UNICEF Nigeria.
Asali: Facebook

Kabilun da suka fi yara masara zuwa makarantar boko

Jaridar BusinessDay ta ce a Kudancin Najeriya kuma sun haɗa da Kudu maso Yamma da yara 1,146,900, Kudu maso Kudu 431,300, da Kudu maso Gabas 240,200 da ba sa makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta duba kabilun da suka fi yara da ba su zuwa makaranta a Najeriya.

1. Kabilar Hausawa

Rahotanni sun tabbatar da cewa kabilar Hausa, wadda ta kai mutum miliyan 69.2, na da yara miliyan 8.11 da ba su zuwa makaranta, wanda ke wakiltar kashi 11.72.

Jihohin da ke da da kabilun Hausawa sun hada da Kano da Sokoto da Jigawa da Katsina da Kebbi da Kaduna da sauransu.

2. Kabilar Fulani

Fulani sun kasance na biyu a Najeriya a cikin jerin wadanda ba su zuwa makaranta musamman a yankin Arewacin Najeriya da suka fi yawa.

Fulani wadanda suka kai mutum miliyan 25, na da yara 3,305,500 da ba sa makaranta, wanda ya kai kashi 13.2 na yawan su gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Abba ya dauko yaki da talauci gadan gadan, ya raba jarin Naira biliyan 2.1 a Kano

Jihohin Fulani sun hada da Adamawa da Gombe da Yobe da Borno da kuma yankin Arewa Maso Yamma.

3. Ƙabilar Kanuri

Kanuri da suka fi yawa a jihohin Borno da Yobe sun kasance na uku a Najeriya wadanda ke da yara da ba su zuwa makaranta, cewar jaridar Vanguard.

Kanuri na da yawan mutane miliyan huɗu, yayin da yara 982,200 ba su makaranta, wanda ke wakiltar kashi 24.6 na yawan su gaba ɗaya.

4. Kabilar Yarbawa

Kabilar Yarbawa da ke Kudu maso Yamma a Najeriya su ne na hudu a Najeriya da yawan yara marasa zuwa makaranta.

Kabilar na da yawan mutane miliyan 50, daga cikinsu akwai yara 855,700 da ba sa makarantar boko, wanda ke wakiltar kashi 1.7 na yawan su.

5. Kabilar Igbo

Mafi yawan Kabilar Igbo sun fi yawa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da wasu yankunan Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

'Mutum 3927 za a ɗauka': Ƴan Najeriya da suka nemi aikin Kwastam sun haura 573000

Yawan yan Kabilar ya kai mutum miliyan 30, yayin da take da yara 796,600 da ba su zuwa makaranta, wanda ke wakiltar kashi 2.7.

6. Kabilar Tiv

Mafi yawan yan Kabilar Tiv, sun fi yaɗuwa a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya musamman a jihohin Benue da Taraba da Nasarawa da Plateau.

Kabilar Tiv sun kai miliyan 5, dauke da yara 215,900 da ba sa makaranta da ya kai kaso 4.3.

Sauran sun hada da Kabilar Ijaw da yara 132,200 da ba su zuwa makaranta sai Ibibio na da yara 120,000 da ba su zuwa makaranta daga miliyan 4.5 wanda ya kai kaso 2.67.

Legit Hausa ta yi magana da wani Bafulatani kan lamarin

Mohammed Haruna Sajo wanda ya yi makarantar makiyaya (Nomadic School) ya bayyana kalubalen da suke fuskanta.

"Akwai kalubale da yawa musamman ga Fulani dole za a rika samun yawan yaran da ba su zuwa makarantar boko."
"Daman mafi yawanmu ba mu san muhimmancin karatun boko ba, ba mu samun zama a kullum muna cikin kiwo dole mafi yawansu su tsinci kansu a haka."

Kara karanta wannan

'Dan majalisar NNPP, ya fadi abin da Ganduje ya 'shiryawa' jam'iyyar APC a 2027

- Haruna Mohammed Sajo

Sai dai ya ce karatu kowane iri ne yana da muhimmanci musamman a wannan zamani.

Ya shawarci gwamnatoci su mayar da hankali wurin ba al'umma ilimi tun da shi ne ginshikin rayuwa.

Matsalolin rashin zuwa makaranta a Arewa

Kun ji cewa ilimi a Arewacin Najeriya na fuskantar manyan kalubale, musamman rashin tsaro, talauci, da al’adun da ke hana yara zuwa makaranta.

Duk da cewa gwamnati, kungiyoyin kasa da kasa da ma na Najeriya na kokari don magance matsalar, akwai aiki mai yawa a gaba.

Wannan rahoto ya yi bayani kan matsalolin da ilimi ke fuskanta a Arewa, da kuma hanyoyin magance su cikin sauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.