UNICEF Ta Ayyana Najeriya a Matsayin Kasa Mafi Yawan Yara Marasa Zuwa Makaranta

UNICEF Ta Ayyana Najeriya a Matsayin Kasa Mafi Yawan Yara Marasa Zuwa Makaranta

  • Asusun tallafawa ƙananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya koka kan yawaitar yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya
  • UNICEF ta ce matsalar ana yawan samunta ne a yankunan Arewacin Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma da maso gabar
  • Hukumar ta bayyana manyan abubuwan da suke jawo matsalar da hanyoyin da za a bi wajen magance ta ko ƙoƙarin rage mata karfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Asusun kula da ƙananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya ce Najeriya ce ƙasa mafi yawan yaran da ba su zuwa makaranta a duniya.

SCHOOL CHILDREN
UNICEF ta nuna damuwa kan yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya. Hoto: UNICEF Nigeria
Asali: Facebook

Rahoton ya tabbatar da cewa a cikin kashi 100 na yaran Najeriya kashi 60 ne kawai ke zuwa makaranta akai-akai.

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC ya dauki sabon mataki domin kawo karshen wahalar man fetur

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hukumar UNICEF ta koka a kan yadda ake samun yawaitar yara ba basa zuwa firamare da karamar sakandare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya: Adadin yara marasa zuwa makaranta

Bahasin da hukumar ta fitar ya nuna cewa yara miliyan 10.2 ne wadanda suka kai shiga firamare amma basa zuwa makaranta.

Haka zalika akwai yara miliyan 8.1 da suka kai shiga karamar sakandare amma basa zuwa, cewar jaridar Tribune Online.

Kididdigar ta fito ne daga jami'in UNICEF, Dakta Tushar Rane a wani bayani da ya yi lokacin rufe taron masu ruwa da tsaki a kan yaran da basa zuwa makaranta a Gombe.

Taron ya mayar da hankali a kan yadda za a mayar da yara makarantu da tabbatar da suna zuwa akai-akai kuma ya shafi jihohin Gombe, Adamawa da Bauchi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta kuma juyowa kan 'yan Kirifto domin inganta Naira a Najeriya

Hukumar har ila yau ta koka kan yadda ake samun karancin ingantaccen ilimi tsakanin dalibai musamman a yankunan Arewa maso yamma da Arewa maso gabas.

Nigeria: Me yake hana yara zuwa makaranta?

Da yake bayyana dalilan da suke kawo matsalar Dr. Rane ya jingina lamarin da yawaitar talauci. A cewarsa ana samu mafi yawan wadanda basa zuwa makaranta ne daga gidajen talakawa.

Jami'in ya kara da cewa rashin kulawar gwamnati a kan harkar ilimi da ilimantarwa ya yi tasiri sosai wajen kara girman matsalar.

A karshe ya lissafa rashin saka kudin da ya kamata a harkar ilimi, rashin samar da ajujuwan karatu da kwararrun malamai daga cikin laifuffukan gwamnati.

SUBEB za ta horar da malaman makaranta

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar ilimin bai daya ta kasa (UBEC) ta kaddamar da shirin horar da malamai 1,480 daga karkara a fadin Najeriya.

Sakataren hukumar, Dakta Hamid Bobboyi ya ce horon za a yi shi ne domin farfaɗo da darajar harkar ilimi da ilmantarwa musamman a yankunan da suka fi bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel