Yadda 'Yan Boko Haram 129,417 Suka Mika Wuya ga Sojojin Najeriya

Yadda 'Yan Boko Haram 129,417 Suka Mika Wuya ga Sojojin Najeriya

  • Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa dubban 'yan Boko Haram da iyalansu sun mika wuya a bana
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan Boko Haram kusan 130,000 da suka hada da mayaka, matansu da yara ne suka mika wuya
  • Janar Musa ya bayyana cewa dabarun hadin gwiwar sojoji da wasu matakai da suka dauka sun taimaka wajen cimma nasarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Qatar - Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana nasarar da sojoji suka samu wajen shawo kan matsalar tsaro.

Janar Christopher Musa ya yi bayanin ne yayin taron tsaro karo na 18 da aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar.

sojoji
Boko Haram 129,417 sun mika wuya ga sojoji. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa taron ya samu mahalarta daga kasashen Najeriya, Guinea Bissau, Gambia, Afrika ta Kudu, Kenya, da Qatar.

Kara karanta wannan

An kama 'yan ta'addar da suka tunkari kasuwa da bindigogi domin kai hari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Boko Haram 129,417 sun mika wuya

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce 'yan Boko Haram 129,417 ne suka mika wuya ga sojoji daga watan Yuni zuwa Disamba.

Daily Post ta ruwaito cewa wadanda suka mika wuyan sun hada da mayakan 'yan ta'addar 30,426, matansu 36,774 da kuma yaransu 62,265.

Hafsun tsaron ya ce yawan wadanda suka mika wuya daga Boko Haram ya nuna tasirin dabarun hadin gwiwar yakin sojojin Najeriya.

Gudunmawar sojoji ga cigaban tattalin arziki

Janar Musa ya bayyana cewa nasarorin da suka samu sun samar da dama wajen habaka tattali a yankuna bayan samar da zaman lafiya.

Ya kara da cewa ayyukan tsaro da suke sun taimaka waje rage kai hare-hare wuraren da ake hakar mai wanda hakan ke shafar tattali kai tsaye.

A karshe, hafsun tsaron ya yaba wa irin rawar da jami’an tsaro suka taka wajen tabbatar da ganin an samu zaman lafiya a Najeriya, wanda ke kara karfafa gwiwar ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

Makiyaya sun kwace bindigar wani babban soja, an cafke shugaban Miyetti Allah

An kama dan bindiga mai raba makamai

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta rushe mafakar 'yan ta'adda a karamar Bassa ta jihar Filato tare da cafke wani dan bindiga mai suna Mamman.

Sojojin Najeriya sun kama abokin ta'addancin Mamman, Alhassan Samaila, kuma suka kwato tarin harsasai da suka boye a mafakarsu da aka wargaza.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng