Shugaban ‘Yan Sanda Ya Aika Sabon AIG zuwa Kano Ana Tsakiyar Rikicin Masarauta
- Sufeta Janar na ‘Yan sandan Najeriya ya yi nadin sababbin AIG da za su canji wadanda suka yi ritaya a shiyyoyi
- IGP Kayode Egbetokun ya amince AIG Ahmed Ammani ya maye gurbin AIG Ari Mohammad Ali da aka nada a Satumba
- Ammani ya zo lokacin da aka gaza kawo karshen rikicin masarauta da ake ciki bayan dawod a Muhammadu Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Sufeta Janar na ‘Yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi nade-naden manyan mataimakan sufeta a kasar nan.
IGP Kayode Egbetokun ya tura manyan jami’an AIG da za su jagoranci wasu shiyyoyi da kuma sashen binciken manyan laifuffuka.

Asali: Facebook
The Nation ta wallafa cewa Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya sanar da haka a cikin makon nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda: IGP ya nada sababbin AIG
Sababbin mataimakan Sufeta Janar da aka tura sun hada da AIG Suleiman M. Yusuf wanda aka aika shiyya ta 9 (Umuahia) a Abia.
Shi kuma AIG Ahmed Ammani ya karbi aikin shiyya ta I (Kano) sai AIG Zachariah Fera ya tafi shiyya ta 4 (Makurdi) a jihar Benuwai.
Sanarwar ta ce wanda za ta shugabanci sashen binciken manyan laifuffuka da ke Onikan a jihar Legas ita ce AIG Augustina Ogbodo.
Shugaban 'yan sanda ya ja kunnen sababbin AIG
A daidai lokacin da ake rikicin masarauta a Kano, Egbetokun ya gargadi sababbin jami’an da aka tura da su guji aikata ba daidai ba.
Shugaban ‘yan sandan kasar ya bukaci su rika sa ido da kyau wajen aikinsu tare da tabbatar da cewa sun gujewa sabawa dokokinsu.
Shi AIG Suleiman Amuda ya canji AIG Echeng Eworo Echeng wanda ya yi ritaya, zai jagoranci jihohin Abia, Ebonyi da kuma Abia.
Kwamishinan 'yan sanda ya hadu da AIG
Daily Post ta rahoto cewa kwamishinan ‘yan sandan Kano, Salman Dogo Garba ya ziyarci AIG Ahmed Ammani da aka turo yankin.
CP Dogo Garba ya taya AIG Ahmed Ammani lale da zuwa jihar Kano, ya na mai yi masa fatan samun nasarar magance rashin tsaro.
Shugaba Tinubu ya yi nadin mukamai
A yammacin Juma'a aka ji labari cewa kwanaki kadan da dawowa Najeriya, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da yin nadin mukamai.
Shugaban Najeriyar ya canza Sanata Sani Yahaya Kaura da Hon. Abdulkadir S. Usman a NWDC kuma an yi wasu nadi a hukumar SEDC.
Asali: Legit.ng