Ana Tsaka da Rigimar Sarauta a Kano, Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatar da Muhuyi Magaji

Ana Tsaka da Rigimar Sarauta a Kano, Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatar da Muhuyi Magaji

  • Kotun Daukaka Kara a Abuja ta wanke shugaban hukumar hukumar karɓar korafe-korafe da rashawa a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado
  • Kotun ta ce kwata-kwata matakin da kotun da'ar ma'aikata ta CCT ta yi ya saba ka'ida kuma bai inganta ba
  • Wannan na zuwa ne bayan dakatar da Muhuyi Magaji a ranar 4 ga Afrilun 2024 sakamakon zarge-zargen da hukumar CCB ta yi masa kan rashin da’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta rushe dakatarwar da aka yi wa shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da rashawa a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.

Hukuncin ya biyo bayan yanke shawarar wani kwamitin alkalai uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Umaru Fadawu.

Kotu ta rusa dakatar da Muhuyi Rimingado da aka yi
Kotu a Abuja ta wanke shugaban hukumar yaki da cin hanci a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado. Hoto: Muhuyi Magaji Rimingado.
Source: Facebook

Dakatar da Muhuyi Rimingado daga muƙaminsa

Channels TV ta ruwaito cewa kotun ta bayyana dakatarwar da kotun da'ar ma’aikata (CCT) ta yi a matsayin rashin adalci da tauye hakkokin Rimingado.

Kara karanta wannan

Mata ta jawo kotu ta tasa keyar dan takarar gwamna da mutane 3 gidan kaso, ta jero dalilai

An dakatar da Muhuyi Magaji a ranar 4 ga Afrilun 2024 sakamakon zarge-zargen da hukumar da'ar ma'aikata (CCB) ta yi masa kan rashin da’a.

Alƙalin da ya yanke hukuncin, Danladi Umar a wancan lokaci ya shawarci Abba Kabir da sakataren gwamnatinsa su nada sabon shugaban hukumar.

Umar ya ce nada mukaddashin shugaban hukumar zai ba da damar kammala bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Rimingado.

Kotu ta wanke Rimingado kan dakatar da shi

Sai dai Mai Shari’a Fadawu ya ce matakin da CCT da dauka bai inganta ba kuma ya sabawa ka'idojin adalci, cewar Tribune.

“Dakatarwar da CCT ta yi bai inganta ba kuma ya sabawa ka’idojin adalci na sauraron shari’a."
"Mun kuma bayar da umarnin cewa a sake tura shari’ar zuwa wani kwamitin daban na kotun.”

- Umaru Fadawu

Kotu ta bukaci korar Rimingado daga muƙaminsa

A baya, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yi zama kan tuhume-tuhume da ke kan Muhuyi Magaji Rimingado.

Kara karanta wannan

Bayan fafutukar shekaru 22: Kotu ta ba malamin da aka kora a aiki nasara

Kotun ta umarci sallamar shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da rashawa a Kano saboda saba umarnin kotu da ya yi bayan kararsa da ake kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.