Kano: Rimingado Ya Sha Alwashin Sake Binciko Badakalar Ganduje Akan Daloli, Ya Yi Alkawarin Kau Da Cin Hanci

Kano: Rimingado Ya Sha Alwashin Sake Binciko Badakalar Ganduje Akan Daloli, Ya Yi Alkawarin Kau Da Cin Hanci

  • Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci (PCACC) a jihar Kano, Muhuyi Rimingado ya sha alwashin ci gaba da binciken tsohon Gwamna Ganduje
  • Ya bayyana haka yayin wata hira da 'yan jaridu a ranar Laraba 21 ga watan Yuni bayan dawo da shi kujerarsa
  • Ana zargin Ganduje ya dakatar da shi ne saboda bincikensa akan wasu kwangiloli da suka shafi iyalansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Jama'a da Yaki da Cin Hanci (PCACC) a jihar Kano, Muhuyi Rimingado ya sha alwashin ci gaba da binciken tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Muhuyi ya ce binciken zai ta'allaka ne akan badakalar Daloli da aka ga gwamnan a wani faifan bidiyo na karba daga wurin 'yan kwangila yana durawa a aljihunsa.

Rimingado ya sha alwashin binciko badakalar Ganduje a bidiyon Daloli
Muhuyi Rimingado Da Tsohon Gwamna Ganduje Na Jihar Kano. Hoto: Hausa Legit.
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Gwamna Abba Kabir a ranar Laraba 21 ga watan Yuni ya dawo da Muhuyi kujerarsa bayan dakatar da shi da tsohon gwamna ya yi.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Aike da Sako Ga Tinubu, Ya Nemi Ya Binciko Badakalar CBN Tun Lokacin Sanusi

Muhuyi ya sha alwashin binciko badakalar Daloli

Daily Nigerian ta ce dakatarwar ba ta rasa nasaba da bincikar badakalar da Muhuyi ya ke yi akan wasu kwangiloli da tsohon gwamnan ya bai wa iyalansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da ya ke hira da 'yan jaridu, Rimingado ya sha alwashin binciko badakalar Daloli da kuma dagewa wurin ganin ya dakile cin hanci a jihar.

A cewarsa:

"Na ji dadi yadda gwamnati ta bi umurnin kotu wurin dawo da ni kujerata, kuma na ji dadin yadda mutane suke turo sakon taya murna.
"Hakan shi ya ke tabbatar da cewa mutane sun ji dadin aikin da muka yi a baya, kuma ina mai tabbatar da cewa zamu kara kokari sosai."

Ya ce ba zai gajiya ba wurin ganin ya dakile cin hanci a jihar Kano

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Ya kara da cewa:

"Kamar yadda na ce kafin a dakatar da ni, muna binciken bidiyon, kuma zamu ci gaba da binciken yanzu ma, duk sauran abubuwa da mutane suke tsammanin an manta da su zamu dawo mu ci gaba da bincikensu."

Ya ce duk da matsalolin da ya fuskanta a baya, ba zai gajiya ba don ganin ya kauda cin hanci a jihar.

Kano: Abba Kabir Ya Mayar Da Muhuyi Kan Muƙaminsa Na Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dawo da Muhuyi Rimingado a matsayin shugaban Karbar Korafe-korafen Jama'a da Yaki da Cin Hanci.

Gwamnan ya dawo da shi ne bisa umarnin kotu da ta bayar, inda ake zaton zai ba shi daman karisa binciken da ya fara.

Sanusi Bature, babban sakataren yada labarai na gwamnatin Kano, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel