Gwamna Radda Ya Amince da Mafi Karancin Albashi, Ya Fadi Abin da Zai Biya Ma'aikata
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya sanar da amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata
- Dikko Radda ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar bayan an kammala tattaunawa
- Gwamna Radda ya bayyana cewa za a fara biyan sabon tsarin albashin ga ma'aikata daga watan Disamban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Gwamna Radda ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar Katsina.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Gwamna Radda ya sanya a shafinsa na X safiyar ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Radda ya amince da mafi ƙarancin albashi
Gwamna Radda ya bayyana ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin ne bayan an kammala tattaunawa a kansa cikin nasara.
Ya bayyana cewa za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ne daga watan Disamban 2024 a faɗin jihar.
Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa ƙarin albashin zai shafi ma'aikata a kowane ɓangare da suka haɗa da jiha, ƙananan hukumomi da hukumar kula da ilmi ta ƙananan hukumomi.
Gwamnan Katsina, Radda ya godewa ma'aikata
Ya kuma nuna godiyarsa ga ma'aikatan jihar kan haƙurin da suka nuna.
"Barkanmu da safiya Katsinawa, bayan tattaunawa mai inganci cikin nasara kan sabon mafi ƙarancin albashi na kasa, ina mai farin cikin sanar da amincewa da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi."
"Wannan kuma zai kasance tare da daidaita albashin ma’aikata a kowane ɓangare, ciki har da jihohi, ƙananan hukumomi, da hukumar Ilimi ta ƙananan hukumomi, daga Disamba 2024."
"Ina miƙa matuƙar godiyata ga ma’aikatan gwamnati bisa haƙuri da fahimta da suka nuna."
- Dikko Umaru Radda
Gwamna Radda ya yi abin a yaba
Wani malamin makaranta mai suna Musa Sani ya bayyana Legit Hausa cewa gwamnan ya yi ƙoƙari bisa amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi.
Sai dai, ya bayyana cewa ƙarin ba wani abin a zo a gani ba ne ga ma'aikata waɗanda suka wuce mataki na bakwai.
"Eh gaskiya abin a yaba ne abin ds ya yi, amma sai dai ba mu yin farin ciki domin da na duba na ƙarin da aka yi, ba wani abin a zo a gani ba ne duba da yadda rayuwa ta yi tsada."
"Wannan ƙarin dai kawai waɗanda ke a matakin ƙasa ne za su ji daɗinsa."
- Musa Sani
Gwamna Radda ya gabatar da kasafin kuɗi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gabatarwa majalisar dokokin jihar kasafin kudin shekarar 2025.
Gwamna Dikko Radda ya gabatar da N682,244,449,513.87 a matsayin kasafin kudin jihar Katsina na shekarar 2025 mai zuwa.
Asali: Legit.ng