Majalisar Dattawa Ta Tafka Muhawara, Kudirin Harajin Tinubu Ya Tsallake Karatu na 2
- Majalisar Dattawa ta amince kudirorin sake fasalin haraji sun tsallake karatu na biyu a zaman yau Alhamis, 28 ga watan Nuwamba
- Sanatoci sun yi muhawara kan kudirin bayan jawabin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele
- Gwamnonin da ke mulki a jihohin Arewa da sarakuna sun yi fatali da kudirin, inda suka nemi shugaban kasa ya sauya tunani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar Dattawan ta yi muhawara kan sababbin kudirorin sauya fasalin haraji guda huɗu da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aiko mata.
Kudirin harajin wanda ya tada hayaniya a sassan kasar nan ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa yau Alhmis, 28 ga watan Nuwamba.
Majalisa ta yi muhawara kan kudirin haraji
Daily Trust ta ce hakan ya biyo bayan jawabin da shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta Tsakiya) ya yi kuma sanatoci suka tafka mahawara a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jiya Talata wasu manyan jami'an gwamnatin Tinubu suka bayyana gaban majalisar inda suka yi mata karin bayani kan ainihin manufar ƙudirin.
Wannan kudiri na sauya fasalin haraji ya tada kura a sassan Najeriya, inda manyan mutane suka soke shi tare da kira ga shugaban ƙasa ya canza shawara.
Yadda kudirin haraji ya tada ƙura
A baya dai gwamnonin Arewa, da sarakunan gargajiya, da kungiyar dattawan Arewa sun yi watsi da kudirin.
Har ila yau, majalisar tattalin arziki ta ƙasa watau NEC ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ta bukaci Tinubu ya janye kudirin.
To sai dai duk da waɗannan kiraye-kiraye da shawarwari, Shugaba Bola Tinubu ya ƙafa cewa ba zai canza ra'ayi ba domin ya hango alheri a tattare da kudirin.
A yanzu dai bayan muhawara a kansa, majalisar dattawa ta miƙawa kwamitin kula da harkokin kudi domin yin abu na gaba wanda ya haɗa da jin ra'ayoyin jama'a a cewae rahoton NTA.
Majalisar dattawa ta ba Kawu Sumaila muƙami
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Kawu Sumaila daga jihar Kano ya samu mukamin shugaban kwamitin albarkatun mai a Majalisar Dattawa.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio shi ya nada Kawu Sumaila domin maye gurbin marigayi Sanata Ifeanyi Ubah da ya rasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng