Hatsarin Jirgi: An Samu Karin Gawar Ma'aikacin NNPCL bayan Kwanaki
- JamOfishin binciken tsaron Najeriya ya tabbatar da cigaba da aikin zakulo gawargwakin wadanda su ka mutu a hadarin jirgin sama
- Wani jirgi mai saukar ungulu da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya dauko haya ya fadi a garin Fatakwal da ke jihar Ribas a makon jiya
- Daraktar hulda jama'a da kare hakkin abokan hulda, Bimbo Oladeji ta ce an gano karin gawa guda wanda aka kai dakin adana gawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Ofishin binciken ba da kariya (NSIB) ya sanar da gano karin gawar mutum guda da hatsarin jirgin sama ya rutsa da su da jihar Ribas.
Jirgin saman mai dauke da mutane takwas ya tashi ne daga Fatakwal zuwa FPSO - NUIMS ANTAN, inda aka samu mummunan hatsarin.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa daraktar hulda jama'a da kare hakkin abokan hulda, Bimbo Oladeji ta sanar da yadda aka yi nasarar gano karin gawa daga baraguzan jirgin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana aikin nemo gawarwakin ma'aikatan NNPCL
Daily Post ta tattaro cewa Ofishin binciken tsaron kasar nan ya gano gawa ta biyar daga inda jirgi da ke dauke da ma'aikatan NNPCL ya fadi.
Daraktar hulda jama'a da kare hakkin abokan hulda, Bimbo Oladeji ta ce ta tabbatar da haka a sanarwar da ta fitar ranar Laraba.
An gano gawa daga hadarin jirgin NNPCL
Ma'aikata da ke cigaba da aikin ceto a jihar Ribas sun kara samun gawar mutum daya daga hadarin jirgin da NNPCL ya dauko haya, amma ba a kai ga fadin waye ba.
NSIB ya ce ma'aikata na musamman ne su ka dauko gawar saboda yanayin da ta ke ciki, kuma an mika ta dakin adana gawa.
Ma'aikatan NNPCL sun yi hadarin jirgin sama
A wani labarin kun ji cewa hatsarin jirgin sama ya rutsa da wasu ma'aikatan kamfanin mai na kasa (NNPCL) a jihar Ribas inda aka shiga rudani bisa fargabar rasuwar fasinjojin jirgin.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin sufurin jiragen sama, Odutayo Oluseyi ya tabbatar da cewa jirgin mai saukar ungulu ta fadi a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers a ranar Alhamis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng